Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta gurfanar da gwamnonin jihohin Nijeriya da mataimakansu da sauransu a gaban kuliya a kan laifukan r ikice-rikicen zabe, cin hanci, sayen kuri’u, da kuma hada baki wajen aikata laifuka a lokacin zaben 2023.
Haka kuma kotun ta umurci INEC da ta tabbatar da shirya lauyoyinta da za su binciki shari’ar rikice-rikicen zabe da sauran laifukan zabe da ake zargin gwamnonin jihohi da mataimakansu da aikatawa a zaben 2023.
- INEC Ta Yi Wa Jam’iyyun Siyasa Gori A Kan Rajistar Mambobi
- Akwai Yiwuwar Majalisa Ta Gyara Tsarin Mulki Don Bai Wa INEC Damar Zaben Kananan Hukumomi
Sannan kuma kotun ta umurci INEC da ta gaggauta yin bincike kan rikicin zabe da sauran laifukan zabe da aka yi a 2023 da kuma gano wadanda ake zargi da aikata laifuka da masu daukar nauyinsu tare da tabbatar da gurfanar da su a gaban kotu.
Mai shari’a Obiora Egwuatu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis da ta gabata biyo bayan wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/583/2023, wadda kungiyar kare hakkin Dan’adam da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta shigar a gaban kotun.
Mai shari’a Egwuatu ya kuma umurci INEC ta gaggauta gurfanar da duk wadanda aka kama a zaben 2023 da ke hannun hukumar ‘yansandan Nijeriya, hukumar yaki da yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC) da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaka da hukumomin tsaro.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Egwuatu ya ce, “Na yi matukar tantance bayanan da ke cikin takardar shaidar SERAP, kuma ba ni da wani dalilin da zai hana in yarda da bayanan idan aka samu hujjojin da ke tabbatar da bayanan.”
Mai shari’a Egwuatu ya kuma bayyana cewa, “A halin da ake ciki, na tabbatar da gaskiya a cikin karar. Batu daya tilo na ko ya kamata wannan kotu ta ba da sassauci ga sake duba shari’a da bayar da umarni kan nasarar SERAP. Don haka, ina tabbatar da wannan hukunci.”
A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 20 ga Yuli, 2024 da ta aike wa, shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu kan hukuncin, mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce, “Muna rokonku da ku yi kokarin bin doka da oda cikin gaggawa na yin biyayya da wannan hukuncin kotun.”
A cikin wani bangare na wasikar da SERAP ta rubuta, “Muna rokonka da ka tunkari alkalin-alkalan tarayya kamar yadda karkashin sashe na 52 na dokar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka masu alaka da su don ba da izini ga lauyoyi kan binciki shari’ar laifukan zabe da ake tuhumar gwamnoni da kuma mataimakansu a lokacin zaben 2023, kamar yadda kotu ta umarta.
“Muna kuma bukatar ku yi aiki kafada da kafada da rundunar ‘yansandan Nijeriya, hukumar yaki da yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC), hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin laifuka masu zaman kansu da sauran jami’an tsaro domin gurfanar da wadanda suka aikata laifukan zabe da kuma masu daukar nauyin laifukan zabe a zaben 2023, kamar yadda kotu ta umarta.
“Tabbatar da aiwatar da hukuncin da INEC za ta yi nan take zai zama nasara ga bin doka da oda, adalci da kuma kubutar da zabukan Nijeriya daga fadawa rikice-rikice. Haka kuma za ta karfafa ‘yancin ‘yan Nijeriya wajen shiga harkokin gwamnatin.
“Ta hanyar bin hukuncin, za ku nuna wa ‘yan Nijeriya cewa hukumar zabe a shirye take wajen kawo karshen rashin hukunta wadanda suka aikata laifukan zabe a kasar nan.
“Aiwatar da hukuncin nan take zai dawo da martaba da amincewar jama’a kan tsarin zaben Nijeriya. Haka kuma za ta tabbatar da bin tsarin kundin mulkin Nijeriya da kuma dokar zabe.
“SERAP ta yi imanin cewa za ku bin wannan hukunci a matsayin babban al’amari na sake fasalin zabe, kuma wata muhimmiyar dama ce ga INEC ta tabbatar da ‘yancinta da ikonta. Don haka muna sa ran samun kyakkyawar amsa da kuma matakin da za ku dauka kan hukuncin.”
Nijeriya dai ta dade tana fama da rikice-rikicen zabuka da cin hanci da rashawa da sayen kuri’u da tasirin da bai dace ba da kuma wasu munanan laifukan zabe.
SERAP ta shigar da karar ne kan kotu ta tilasta wa hukumar zabe ta gudanar da ayyukanta wanda tsarin mulki da doka suka dora mata don tabbatar da gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifukan zabe da masu daukar nauyinsu a zaben 2023.