Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi
Kotun ɗaukaka ƙara dake zaman ta a Sokoto ta warware hukuncin da babbar Kotun dake Jihar Kebbi ta gabatar shekaru biyu da suka shuɗe wanda ta wanke Mohamed Arziƙa Ɗan Atto, tsohon Akanta Janar na Jihar ta Kebbi, a kan zargin da ake yi masa kan amfani da ofishin sa da ya yi zama a matsayin akanta Janar na Jihar Kebbi da kuma haɗin kai domin yin sama da faɗi da kuɗaɗen asusun Jihar Kebbi da suka kai kimanin Naira biliyan 1.6 da ya biya kansa a matsayar kuɗin kwangilar da kamfanin sa ya gudanar a Jihar ta Kebbi wanda hukumar EFCC ta tuhume shi da kuma wani mutum ɗaya a gaban kotun ɗaukaka ƙara da ke garin sakkwato.
Hukumar ta EFCC ta tuhume shi ne a kan amfani da ofishinsa don wadatar da kansa ga kuɗaɗen Jihar Kebbi dasu ka kai nauyin Naira biliyan 1.6.
An zargi Muhammad Arziƙa Ɗan Atto Ɗakingari tare da Alhaji Musa Yusuf, wanda daraktan kamfanin ‘Beal Construction Nigeria Limited’, kamfanin da Ɗan Atto ya yi, kuma ya yi amfani da shi wajen bayar da kwangila daban-daban ga kansa.
Bisa ga binciken da hukumar EFCC ta gudanar daga hukumar harkokin yi wa kamfuna rijista kan harkokin kasuwanci watau CAC ta nuna cewa Mohammed Bashir Mohammed, Anwal Sadat da Nasir Muhammad, duk ‘ya’yan tsohon Akanta Janar ne kuma sune daraktoci masu kula da kamfanin ‘Beal Construction’, yayin da ‘yan uwansa guda biyu da Abdallahi Mohammed da kuma Habibu Mohammed sune sauran daraktoci masu jari a cikin kamfanin da kuma zatas wa ga kamfanin na ‘Beal Construction Limited’.
Kamfanin ya mallakin asusun biyu a Bankin ‘Eco da Unity’ banki tare da Ɗan Atto da kuma Musa Yusufu a matsayin masu sa hannu kan asusun wurin cire kuɗi a banki.
Har ila yau, Ɗan-Atto yana yin aiki biyu ne wurinsa hannu, ɗaya a matsayinsa na akanta Janar kan asusun Jihar kuma ɗayan a matsayin mai shi na kamfanin ‘Beal Construction Limited’.
Haka zalika bincike da hukumar EFCC ta yi kan asusun Jihar ta kebbi ya nuna cewa yawancin Naira Biliyan 1.3 tsakanin watan Mayu na shekara ta 2012 da kuma Satumba na shekara ta 2013, tare da mafi yawan karɓar kuɗaɗen da suka fito daga Ofishin Akanta Janar na jihar ta Kebbi watau Asusun jihar da ma’aikatar kuɗi ta Jihar Kebbi.
Bugu da ƙari wasu daga cikin kwangilar da aka gudanar a cikin jihar, cewa ‘Beal Construction Company’ ya samu mai yawa fiye da duk wani kamfani a duk fannin Jihar ta Kebbi, kwangilar da kamfanin nasa ya gudanar sun haɗa da samar da kujerun zaman ga makarantun sakandare 66 a jihar Kebbi da aka ƙiyasta a Naira Miliyan 987; haɗi da gine-gine da kuma samar da ruwa a babban masallacin na cikin Babban Birnin Jihar ta Kebbi, mai daraja a Naira Miliyan Ɗari Biyu da Miliyan Ɗari da Miliyan Ɗari, da kuma ginin da aka raba a makarantar sakandaren Mu hammadu Mera da aka kai Naira Miliyan Dubu Biyu da Miliyan Ɗari Biyu .
Bayan kammala binciken, ita hukumar EFCC ta gabatar da laifufuka guda 20 ga kotun na ƙulla makirci, ta hanyar cin hanci da cin zarafi a kan ofishin akantan janar da Muhammad Arziki Dan- Atto ya riƙa a lokacin gwamnatin Sa’idu Usman Nasamu Dakingari , hukumar ta EFCC ta gabatar da shi da kuma Musa Yusuf.
Babbar Kotun dake zaman ta a Birnin kebbi ta yanke wa Musa Yusuf hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan kurkuku, yayin da kotun ta wanke Muhammad Arziki Dan- Atto kuma ta sallame shi kan zargin hukumar EFCC ke yi masa tare da Musa Yusuf.
A cikin hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara dake sakkwato ta bayyana a jiya a sakkwato a karkashin jagorancin mai shari’a , Usaini Mukhtar, mai shari’a Muhammad Shuaibu da kuma Mai Shari’a Fredrick Oho, Kotun ta ce; “ta amince da zargin da EFCC ta keyi wa tshon akanta janar na jihar ta kebbi, wanda kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan kurkuku ga kowane zargi da akan gabatar da shi a gaban wannan kotun, kan cewa Arziki Dan- Atto zai je gidan kurkuku shekaru bakwai na ɗaurin kurkuku a kowane zargi guda 10 daga daga cikin waɗanda kotu ta amince da su kan aikata laifin da hukumar EFCC ke tuhumar sa da shi.
Daga nan kotun ta ƙara da cewa, za ya gudanar da zaman gidan kurkukun ne ta hanyar ƙirga su sau ɗaya da kuma tare da bin juna.