Alkalin kotun babbar kotun Jihar Zamfara, Mukhtar Yusha’u, ya yanke wa wani Sadiku Abubakar hukuncin daurin rai da rai a bisa samunsa da laifin yunkurin fashi da makami a karamar hukumar Bungudu.
An yanke wa Sadiqu hukuncin daurin rai da rai bayan mika shi hannun ‘yan sanda.
- 2024: Majalisar Zartaswar Adamawa Ta Amince Da Kasafin Naira Biliyan 225
- Kaduna: Muna Neman Afuwar Kisan Masu Maulidi – Hafsan Sojin Kasa
An yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Da yake zantawa da manema labarai a harabar kotun, mai gabatar da kara, Barista Mansur Lawal, mataimakin darakta mai gabatar da kara na ma’aikatar shari’a ta Jihar Zamfara, ya ce ya yi maraba da hukuncin da kotun ta yanke.
A nasa bangaren, lauyan wadanda aka yankewa hukuncin, Barista Muhammad Ahmad Jamo, wanda shi ne kodineta na hukumar bayar da agaji ta kasa reshen Jihar Zamfara, ya ce hukuncin zai zama izina ga wasu.
Sai dai ya bayyana cewa za su duba yiwuwar daukaka karar.