Kotu ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin daurin rai da rai saboda daukar nauyin kungiyar Boko Haram.
Wadanda ke daukar naunyin Boko Haram din sun hada da Zana Zarama, Modu Aisami, Umar Mohammed da Bunu Kame.
- Kotu Ta Umarci Dawo Da Motoci 50 Da Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Kwashe
- Harin Jirgin Sojin Nijeriya Ya Haifar Da Rudani A Kaduna
A ranar Litinin ne aka yanke musu hukuncin bayan da suka amsa laifin da gwamnatin tarayya ke tuhumar su shi a wat babbar kotun tarayya da ke Dawaki a Abuja.
Yayin da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya jagoranci tawagar lauyoyin gwamnatin tarayya.
Wadanda ake tuhumar sun nemi Mai Shari’a Binta Nyako da Mai Shari’a Emeka Nwite, su yi musu sassauci bayan an karanta musu tuhume-tuhume daban-daban.
A cewar tuhume-tuhumen da Daraktan shigar da kara na hukumar DPPF, Mista M. B. Abubakar ya shigar, daya daga cikin wadanda ake tuhuma, Aisami, ya bayar da kudade ga kungiyar ta’addanci ta hanyar siyan kayan abinci daga hannunsu.
An zargi Aisami da sanin cewa za a yi amfani da kudaden da aka samu daga hada-hadar wajen aikata ta’addanci.
Ya ce aikata laifin ya saba wa sashe na 13(1)(a)(ii) na dokar samar da ta’addanci, 2013.