Kotun daukaka kara da ke Sakkwato a ranar Juma’a ta yi watsi da karar da tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida na jihar Sakkwato, Labaran Lumo Dundaye ya yi a kan kamfanin jaridun LEADERSHIP da wakilin ta na Sakkwato.
Da take yanke hukunci ta manhajar zoom mai shari’a Victoria Nwoye ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun jihar Sakkwato ta yi ta hanyar watsi da karar bakidaya, hukuncin da dukkanin alkalai biyar suka aminta.
- Yadda Yakin Kasashen Ukraine Da Sudan Suka Janyo Karancin Irin Alkama A Jihar Gombe
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 181, Sun Cafke 203 A Cikin Mako Guda – Hedikwatar Tsaro
Dundaye wanda ya shigar da karar a 2016, ya yi karar kamfanin LEADERSHIP a matsayin mai kariya na daya da wakilin LEADERSHIP Hausa, Sharfaddeen Sidi Umar a matsayin mai kariya na biyu a babbar kotun jihar Sakkwato a kan wallafe- wallafen da jaridar ta buga a 2012 yana neman diyar naira miliyan 50 da bayar da hakuri a manyan jaridu uku.
A hukuncin babbar kotun a Yuni 2022, mai shari’a, Malami Umar Dogo- Daji ya bayyana cewar mai karar ya kasa gamsar da kotu da gamsassun hujjoji kan bata sunan da ya zargi masu kariya sun yi masa a wallafe- wallafen da LEADERSHIP Hausa ta buga a 2012 da 2015 kan zaben NUJ.
Alkalin ya ce a duka wallafe- wallafen uku da suka shafi zaben kungiyar’yan jarida reshen jihar Sakkwato, mai karar ya kasa bayyana ainihin bata sunan da aka yi masa, hasalima ya bayyanawa kotu maimakon kimarsa ta zube, karin matsayi ya samu bayan wallafe- wallafen.
Tun da farko an fara sauraren karar ne a gaban babban mai shari’a na jihar Sakkwato, Bello Abbas a Fabrairu 2016 wanda ya kori karar a Afrilu 2016 wadda mai karar ya sake shigarwa. Shari’ar ta sake dawowa sabuwa bayan ritaya daga aiki da babban alkalin ya yi a 2018.
Da yake bayani bayan kammala hukuncin, lauyan mai kariya na biyu, Simon Enojo King ya bayyana cewar kotun ta yi abin da ya dace ta hanyar tabbatar da gaskiya da adalci.