Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da zaben Hyacinth Alia a matsayin gwamnan jihar Benuwe.
Idan dai za a iya tunawa, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, Titus Uba ya garzaya kotun daukaka kara inda ya nemi kotun da ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben da ta tabbatar da zaben Alia na Jam’iyyar APC.
- Sanata Ya Biya Wa Dalibai 308 Kudin Makaranta A Adamawa
- Yaki Da Cin Zarafin Mata Na “EU-UN Spotlight Initiative”: Mun Samu Gagarumin Ci Gaba A Legas – Ibijoke
A kotun sauraron kararrakin zaben, Uba da wasu sun yi zargin cewa, mataimakin Alia, Samuel Ode, ya gabatar da takardar shaidar jabu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wanda hakan ya sabawa sashe na 182(1)(j) na kundin tsarin mulikn Tarayyar Nijeriya, na 1999 (wanda aka gyara).
Wani kwamitin mutane uku na kotun sauraron kararrakin zaben karkashin mai shari’a Ibrahim Karaye, ya yi watsi da karar a kan cewa, kotun bata da hurumin sauraron korafin kafin zabe.
Da yake yanke hukunci a kotun daukaka karar a ranar Litinin, kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara karkashin jagorancin Mai shari’a Onyekachi Aja Otisi, ya ce Uba ya kasa tabbatar da zarge-zargen takardun jabun da yace Ode ya gabatar wa INEC.