Kotun koli ta tabbatar da zaben Alex Otti a matsayin gwamnan Jihar Abia a zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
A hukuncin da ta yanke wanda mai shari’a Uwani Abba-Aji ya karanta, kotun kolin ta ce karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Cif Okey Ahiwe, da takwaransa na jam’iyyar APC, Cif Ikechi Emenike, suka shiga ba ta cancanta ba.
- Saraki Ya Taya Gwamnonin Da Suka Yi Nasara A Kotun Koli Murna
- Kotun Koli Ta Ayyana Muftwang A Matsayin Halastaccen Gwamnan Filato
A cewar kotun kolin, hujjar masu shigar da kara na cewa Otti ba dan takarar jam’iyyar LP ba ne a lokacin zaben gwamna ba ta da tushe balle makama, duba da sashe na 177(c) na kundin tsarin mulkin 1999.
Kotun ta yi watsi da batun cewa sunan Otti ba ya cikin jerin sunayen mambobin jam’iyyarsa.
Hakan ya sa kotun ta yi watsi da karar jam’iyyun adawar tare da tabbatar da Otti a matsayin halastaccen Gwamnan jihar.