Kotun kolin ta tabbatar da Dauda Lawal Dare a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara a zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 11 ga watan Maris.
Alkalin kotun mai shari’a Adamu Jauro ne ya jagoranci, kwamitin alkalai biyar, ya yi watsi da karar da wani dan takarar gwamna, Dakta Ibrahim Gusau ya shigar kan zaben.
- Sin Na Ci Gaba Da Dukufa Kan Bude Kofa Ga Ketare
- Wani Soja Ya Hallaka Kwamandansa Ya Kuma Bindige Kansa Da Wasu Sojoji 2 A Sokoto
Ta tabbatar da abin da Mista Damian Dodo SAN, lauya ga Lawal Dare ya gabatar cewa an gabatar da wanda yake karewa bisa doka.
Jauro ya amince da hukuncin kotun daukaka kara da ta amince da zaben fidda gwani na biyu da ya samar da dan takarar.
A zaben fidda gwanin dai Lawal Dare ya samu kuri’u 442 inda ya samu nasara a kan Gusau da sauran ‘yan takara.
Jauro ya ce wata babbar kotun tarayya da ke Gusau wadda ta soke zaben fidda gwani har sau biyu ba ta da hurumi a lokacin da ta yanke hukunci kan karar da Gusau ya shigar.
Zaben fidda gwani na gwamnan PDP na farko da aka gudanar a ranar 25 ga Mayu, 2022 an kalubalanci shi a wata babbar kotun tarayya da ke Gusau kuma ta soke shi.
A hukuncin da babbar kotun ta yanke ta bayar da umarnin sake gudanar da sabon zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 23 ga Satumba, 2022 amma kuma kotun ta soke shi saboda wasu kurakurai.
Bai gamsu da hukuncin babbar kotun ba, Dauda Lawal-Dare, Adamu Maina-Waziri, shugaban kwamitin zaben fidda gwani; sannan Kanar Bala Mande mai ritaya ya garzaya kotun daukaka kara domin neman tazarce.
Wadanda suka amsa karar sun hada da Dakta Ibrahim Shehu-Gusau, Alhaji Wadatau Madawaki, Hafiz Nuhuche da kuma Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
A cikin hukuncin da aka yanke wanda mai shari’a Abubakar Talba a madadin wasu ya karanta, kotun daukaka kara ta ce wadanda suka shigar da kara sun yi nasarar tabbatar da dukkanin wasu dalilai guda bakwai na daukaka kara da lauyoyinsu suka yi masa, kuma kotun ta yanke hukuncin ga abin da ya dace.
Talba ya yi watsi da duk wani yunkuri na farko kan cancantar karar bisa tanadin shari’a da kuma sha’awar sauraren shari’a, yana mai cewa gazawar fasaha ba za ta iya maye gurbin tanadin shari’a ba.
Ya ce alkalin babbar kotun ya yi kuskure kan takardun rangwamen da INEC ta gabatar kuma kotun ba ta ayyana lokacin sake gudanar da zabe da kuma sanarwar shiga zabe ba.