Hausawa na cewa, “Mai nema na tare da samu”, a ranar 3 ga watan Satumban 2025, Sinawa yara da manya, samari da ’yan mata ta ko ina sun cika da farin cikin tunawa da wannan rana mai dimbin tarihi a rayuwar Sinawa, ita ce ranar da aka samu nasara a yaki da zalunci da danniya na Japanawa da suka mamaye yankunan Sinawa.
A bana, Sinawa na murnar cika shekaru 80 da samun wannan babbar nasara wacce juriya, jajircewa da hadin kai ya samar da ita bayan kai ruwa rana, wanda hankali ke dimauta da irin yadda aka cimma wannan nasara.
Saboda muhimnancin wannan rana, fiye da shugabannin kasashen waje 20 ne suka halarci bikin a dandalin Tian’anmen a birnin Beijing, wanda ya cika makil da jama’a, ga kuma an masa ado da kambun tarihin shekarar nasara “1945” da “2025”.
A wannan rana mai dimbin tarihi, rundunar soji ta jama’ar Sin ta gwangwaje duniya da fareti mai kayatarwa tare da baje kolin makamai masu linzami na zamani, jiragen yaki na sama da na ruwa, da sauran kayayyakin yaki na zamani don tunawa da wannan rana ta ’yan mazan jiya.
Yakin duniya na II shi ne mafi muni a tarihin yakin da dan adam ya taba yi. A duk duniya, mutane miliyan 70 zuwa 85 ne suka rasa rayukansu. An yi asarar kusan dala tiriliyan 4. A kasar Sin, shekaru 14 da aka shafe ana gwabzawa da jama’ar kasar Sin kan adawa da danniyar kasar Japan, ya yi sanadin jikkatawa da mutuwar sojoji da fararen hula fiye da miliyan 35, wannan sama da kashi daya cikin ukun wadanda suka mutu a yakin duniya II ke nan. Lallai sannu Sinawa, wato ko za a kare gaba daya, babu guduwa kuma ba mika wuya. A nan ne bahaushe ke cewa, “kowa ya ci zomo, ya ci gudu”.
Yakin ya farkar da Sin da duniya baki daya, wanda ya zama tushen kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, daga bisani kuma ya dora kasar bisa tafarkin zamani. Ga duniya, mulkin mallaka ya fara wargajewa. Kasashe da dama sannu a hankali suka fahimci cewa, in sun jajirce, za su samu ‘yancin kai.
Tasirin yaki da zalunci da danniya da Jama’ar Sinawa suka yi, ya sa kasar ta kudiri aniyar yaki da zalunci da danniya a duniya ta rungumi manufar tabbatar da zaman lafiya, inda ta nuna wa duniya cewa, lokacin wariya da danniya, tsarin rayuwar dabbobi (na sama ya buge na kasa), ba zai dore ba amma samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro, na sama ya yi wa na kasa adalci, shi ne tsarin da ya dace kowa ya runguma.
Wannan fareti na nunawa duniya cewa, sojojin jama’ar kasar Sin an tanade su ne don tabbatar da zaman lafiya da aminci, inda yake a rubuce jikin alluna da tutoci, “Adalci zai yi nasara,” “samar da zaman lafiya zai yi nasara,” da kuma “mutane za su yi nasara”.
Daga cikin kasashe biyar na dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), kasar Sin ta ba da gudummawar mafi yawan dakarun kiyaye zaman lafiya a fadin duniya.
A ’yan kwanakin nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping a lokacin wani taron tattauna bukatun tsarin shugabancin duniya, ya yi nuni da cewa, kasar Sin za ta yi aiki kafada-da-kafada da kasashen duniya domin samar da “tsarin shugabanci na duniya mai adalci da daidaito”.
Wannan ya tabbatar da cewa, yakin da jama’ar Sinawa suka yi a kan yakin zalunci da danniya daga Japanawa bai tsaya nan kadai ba har ma da neman wa sauran kasashe masu tasowa ’yancin zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp