Kowa Ya Yi Ta Kansa, An Sace Sarki A Kaduna

Sulaiman Bala Idris

A shekarun baya kaɗan, ba wai da nisa sosai ba, ina son yin tafiyar dare. Tun kafin na fara tuƙi, ma’ana tun ina hawa motar kasuwa. Daga Kano zuwa Kaduna, daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.

Akwai watarana, ina Kano da misalign karfe 2:00 na rana aka kira ni na zo Abuja, sai bayan ƙarfe 4:00 na yamma sannan na kammala shirin barin Kano. Na bar Kaduna wuraren ƙarfe 8:00 na dare. Akwai wata rana da na tafi bar Abuja ƙarfe 11:00 na dare na tafi Kaduna.

Waɗannan misalan na kawo su ne domin nuna yadda rayuwa ta ke kafin a fara tare hanya ana tsintar mutane kamar kaji. Yanzu da hanya ta zama ‘yar lelen ɓarayin mutane, mai hankali ba zai tsaya sai an bashi shawarar kiyaye lokutan yin tafiya ba.

Abin yana da matuƙar ban takaici da sosa zuciya. Kai ka ce baki aka yi wa Nijeriya da gwamnati. Kullum abin gaba yake yi. Wannan a bayyane yake – a baya satar mutane a kan hanya ake yi. Idan ba ka bi hanya ba ka tsira. Itama satar mutane akan hanya a wancan lokacin, matuƙar za ka kiyaye lokuta, shi ma ka tsira.

Misali, a farko-farkon wannan rashin mutunci na satar mutane, akwai wasu lokuta na musamman da a babin shawara ba a so mutum ya bi babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna. Ba a bin hanyar da sanyi safiya sannan ba a bi idan yamma ta fara yi. Waɗannan lokutan a cikinsu ne masu garkuwa da mutane suke fitowa su kwashi ganima.

Sakaci da rashin sanin darajar aiki irin na gwamnati ne ya sa aka kasa daƙile wannan lamarin na sace mutane tun a farkonsa. Domin a lokacin wasu taƙaitattun wurare ne kawai ake tafka ta’asar. Kuma bisa ƙa’idar nan da na lissafa a sama; sai ka hau hanya za a ɗauke ka.

Toh me ya biyo ba? Da gwamnati ta shashantar da abin, ta ƙi ɗaukar mataki da gangan, sai masu satar mutanen suka samu ƙwarin gwiwar faɗaɗa harkarsu ta ‘yan iska. Tunda mutane sun ankare sun fara kiyaye lokutan yin tafiye-tafiye, sai suka koma kowanne lokaci suka bushi iska ma fitowa suke yi. Idan taƙamarka yin taka-tsantsan, ka fito da tsakar rana, sai ka je hanya ka taras da ɓarayin sun kwashe sama da awa guda suna tsince mutane.

Tun farko ya kamata mu rufawa kanmu asiri, mu fito mu yi ta surutu muna taratsi har sai gwamnati ta yi abin da ya dace, ina nufin tun lokacin da ake ta tarwatsa ƙauyuka a Jihar Zamfara, ana tada ƙauyukan mutane a Katsina da Sakkwato ya kamata a farga.

Ɗabi’a ce ta mutum, musamman mugu irin ɓarawon mutane ko mai cutar da jama’a, har idan zai aikata wata ɓarna a ƙi daƙile shi kwaf ɗaya, toh zai matsa gaba ne. Gaba gaba haka dai, kamar yadda muke gani yanzu a Arewa maso yammacin Nijeriya.

An fara a Zamfara, mun yi tsit muna tunanin cewa lamarin iyaka wasu manoman ƙauye ne ya shafa a Jihar Zamfara. Suka matsa suka shiga wasu ƙauyukan Katsina, nan ma aka yi shiru. Suka matsa sakkwato, suka matsa Neja. Dama ita Jihar Kaduna, ‘yan bindiga sun daɗe suna rarumarta ta gefe, ta ɓangaren Birnin Gwari.

Ɓarayi sun gama lalata ƙauyuka, hanyar ma da suke samu suna tare wa suna kwasar mutane an rage bi, shi ya sa suka fara shiga cikin gari. Toh su ina ruwansu? Ai tunda sun samu marasa kan gado a matsayin shugabanni a haka za su yi ta ɓarna.

Cikin makon da ya gabata waɗannan ‘yan iskan ɓarayin sun yi kashe-kashe masu tada hankali a mabanbantan wurare na Jihar Zamfara. Wannan fa ban ma kawo misalign yadda lamarin ya kai ga shigarsu makarantu ba kenan.

Mutanen Jihar Kaduna ne za sub aka tausayi. Shi Gwamna yana ta yekuwar sabunta cikin gari, su kuma ɓarayi suna ta fasa ginin bulon gidaje suna sace mutane. Idan suka ɓulla Zariya suka ɗiba, sai su leƙa Chikun can ma su kwasa.

Dolenka wannan abin ya tada ma hankali, duk kuwa inda ka ke, ko a birnin Seoul ta Koriya ta Kudu ka ke, idan dai kai asalin ɗan wannan yanki ne na Arewa ta Yamma, kana cike da fargabar rashin sanin wa za a sata kuma a gaba.

Sun je Kajuru sun sace Sarki sukutum guda tare da mutum 12 cikin iyalinsa. Ba fa ‘yan tsaki ba, Sarki aka ce! Wallahi dukanmu muna ruwa, ‘yan uwanmu suna ruwa, sauran al’umma suna ruwa. Wannan abin ya wuce duk yadda ake tsammaninsa.

Wani ya taimaka ya sanar da gwamnatin tarayya da ta jihohin da ake wannan iya shege na sace mutane cewa, ƙiris fa ya rage a kammala kwashe mutanen da za su jefa musu ƙuri’u a zaɓe mai zuwa. Na dai san damuwarsu ba ta wuce a fara kamfen ba – mahaukata!

Exit mobile version