Ku Fatattaki ‘Ya’yanku In Ku Ka Gansu Da Kayan Sata, Buhari Ga Iyaye

Ortom

Wajibi ne duk iyaye, ku matan auren fatattaki yaransu ko mazansu, su mayar da duk wasu kayan alatu da suka san ba za su iya siya ba, inji Shugaban Kasa Buhari. Shugaban kasar ya ce duk wani mutum mai mutunci da daraja ba zai goyi bayan masu warwason dukiyar gwamnati da ta al’umma ba.

Ya ce; aikin shugabannin gwamnati, da na addini da ma na gargajiya ne taruwa wurin yaki da wannan zalama da matasa suke yi a ‘yan kwanakin nan. Shugaban Kasa Buhari ya roki iyaye da su kori yaransu da duk wasu kayan alatu da suka koma da shi gida, wanda sun san ba za su iya siya da kudinsu ba.

Ya sanar da hakan ne bayan zanga-zangar EndSARS ta tsawon sati guda, wacce ta ja bata-gari suka yi ta warwason dukiyar gwamnati da ta al’umma a fadin Nijeriya. Garba Shehu, hadimin shugaban Kasa na musamman, ne ya saki wata takarda a ranar jiya Lahadi, inda Shugaban Kasa ya roki ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da su yi gaggawar tabbatar da zaman lafiya a fadin kasa.

Exit mobile version