Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA), Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci jami’an tsaro su hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi ba tare da la’akari da addininsa ko ƙabilarsa ba.
Ya jaddada cewa ya zama wajibi ’yan ƙasar nan su kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya, su kuma guji rarrabuwa da wasu ke ƙoƙarin haddasawa.
- PDP Ta Ɗage Taronta Bayan Arangamar ‘Yansanda Da ‘Yan Daba A Abuja
- PDP Ba Ta Mutu Ba Duk Da Rikicin Da Ta Ke Fama Da Shi – Anyanwu
Ya bayyana haka ne a yayin bikin taron shekara-shekara karo na 10 na ƙungiyar Muslimi ta Kudu Masu Yammacin Nijeriya (MUSWEN), wanda aka gudanar a Jihar Osun.
Sarkin ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da ’yan ta’adda ke ci gaba da yi a sassan ƙasar nan.
Ya ce an yi maganganu da dama kan batun kisan ƙare dangi, wanda ya ce shi dai bai taɓa ganin ko jin wani Kirista da aka hana ya yi ibadarsa ba, balle har ta kai ga kisa, yana mai jaddada cewa ba za su bari wani ya kawo rabuwar kai a tsakanin ’yan Nijeriya ba.
Sarkin Musulmin, ya kuma roƙi ’yan ƙasar nan da su ci gaba da roƙon Allah Ya ba Shugabanni ikon gudanar da jagoranci yadda ya dace.
Ya taya ƙungiyar MUSWEN murna bisa rawar da take takawa wajen haɗa kai da inganta tattaunawa tsakanin Musulmi a yankin Kudu Maso Yamma, tare da kira ga sauran yankuna su yi koyi.
A yayin taron, an bai wa ɗalibai mata 12 da ke karatun likitanci daga jihohin Kudu Maso Yamma tallafin karatu ƙarƙashin Shirin tallafin karatu na Sultan Abubakar.














