Jarumi a masana’antar Kannywood Haruna Talle Mai Fata ya yi karin haske a kan dalilin da ya sa ya shigo wannan masana’antar ta Kannywood shekaru fiye da ashirin da suka gabata, Haruna wanda dan uwa ne ga Hamza Talle Mai Fata da kuma Baban Umma wadanda dukansu su na wannan harka ta fim ya ce ba suna ya zo nema a Kannywood ba hasalima yanzu haka idan ya samu wata sana’ar da tafi harkar fim kawo kudi zai canza sana’a.
A hirar da ya yi da Hadiza Gabon a cikin shirinta mai suna ‘Gabon’s Room Talk Show’ Haruna ya ce idan zan fada maki abin da ya kawo ni Kannywood zan ce maki kudi ne domin kuwa yadda iyayena suka rufa mani asiri suka rike mani mutuncina haka nima na ke fatan in kiyaye wa ‘ya’yana mutuncinsu.
- Jirgin Ruwan Aikin Jiyya Na “Peace Ark” Ya Kammala Aikinsa A Benin
- Gwamnatin Tarayya Da Google Sun Bullo Da Hanyar Samar Wa Da Matasa 2,500 Aikin Dogaro Da Kai
Babu wata sana’ar da na san zan yi in samu kwabo da ba zan iya yinta ba, don yanzu haka bayan harkar fim ina yin sana’ar ‘recycling’ wato ina sayen tsofaffin robobi in kawo Kano in sayar in samu ‘yan kudadena’’, in ji shi.
Amma fa ba zan taba manta abin alherin da na samu a wannan harka ba domin ta yi mani riga da wando, da kuma sauran abubuwan alherin da na samu ta sanadiyar wannan sana’a, kama daga sanayyar manyan mutane, gida, mota, hajji kai hatta auren da na yi ta sanadiyar wannan sana’a ta fim na yi shi ya kara cewa.
Amma gaskiya neman kudi na zo yi duk da dai na samu daukaka kuma mutane sun sanni da dama,amma idan yanzu zan samu wata sana’ar da zan samu fiye da abinda nake samu a fim kwata kwata zan bar fim in koma waccan sana’ar domin duk abin da zan yi saboda iyalina su samu abin da za su ci a kuma rufawa kai asiri nake yi, inji Haruna.
Da ya ke amsa tambaya dangane da mutanen da ke daukar masu wannan harka ta fim a matsayin yan iska ko wasu mutanen banza Haruna ya ce,ni a kashin kaina duk wani wanda ya ke fadin irin wannan magana walau malami ko almajiri mai kudi ko talaka da duk wani wanda ya ke da irin wannan tunani na cewa yan fim ya iska ne to babu abinda zan ce masu illa su sani akwai ranar da Allah zai taramu ga bakidaya ya yi mana hisabi.
Haruna ya cigaba da cewa babu inda babu dan iska a Duniya kuma babu inda babu mutanen kwarai,kuma kwata kwata babu adalci ka yi wa mutane jam’u yayin da zaka fadi wani abu dangane dasu, ba dukkan malamai ne na kwarai ba hakazalika ba dukkan yan fim ne na banza ba.
Don haka duk wanda ya kiramu da wannan suna na yan iska ko mutanen banza na barshi da mahalicci wanda ya ke da ‘record’ na duk abinda mutum ya yi kuma shi ne yake da ranar sakamako, ranar da babu wani mai dabara ko wayau shi ne zai yi mana hisabi da mu da wadanda ke kiranmu mutanen banza.