Daga Abubakar Abba, Kaduna
Babban Sakatariyar Hukumar tsare-tsare ta Fansho wato (PTAD), Sharon ta bayyana cewar Gwamnati mai ci yanzu ta biya wadanda suka yi ritaya kimanin naira Biliyan 7.5 a matsayin kudin fansho, kamar yadda a yanzu gwamnatin tarayya ta fara tan-tance ‘yan Fansho a Jihar
Legas da nufin gano sahihanci yawan Fanshon da ake bin ta.
Sharon ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi a wata santa a Kotu, bayan ziyar sanya ido akan tan-tance ‘yan fansho santatoci biyar da aka ware don gudanar da tan-tancewar, ta ce, kimanin ‘yan Fansho su 21,000 da gwamnati ta san da zaman su, za a tantance su lokacin tan-tancewar ta sati biyu.
Ta yi nuni da cewar, sakamakon tan-tancewar, tata taimaka wajen sahihin bashin da ake bin gwamnati na kudin fansho da kuma biyan Ariyas din da suka rage.
Babbar Sakatariyar ta ci gaba da cewa, gudanar da tan-tancewar da a yanzu ke gudana a daukacin fadin kasar nan, zata taimaka wajen fuskantar duk wani kalubale da suka hada da samar da biyan fansho alkibla madai-dai ciya da kuma tabbatar da bin ka’ida a tsarin biyan fansho a kasar nan.
Ta kuma koka akan irin mawuyacin kuncin rayuwa da ‘yan fansho a kasar nan suka samu kansu a baya, saboda rashin shigar da sunayen akan tsarin fansho inda hakan ya janyo tsaiko wajen biyan su fansho din su, da kuma tabka nagudi akan tsarin na rashin takardun su.
Ta yi wai waye akan cewar, a shekarar 2016 kimanin ‘yan fansho su 15,000 aka gano basu da lambar tan-tancewa ta (BBN), inda tace, hakan ya haifar babban tsaiko wajen biyan su.
Sharon ta baiwa ‘yan fanshon tabbacin cewar hankokin su zasu fiito bayan an kammala tan-tancewar, ta kuma yabawa gwamnatin jihar Legas akan hadin kai da goyon bayan data bayar, musamman wajen tura motar daukar marasa lafiya da jimi’an kiwon lafiya a cibiyar da ake tantancewar.
A nashi jawabin, Sakataren ‘yan fansho reshen jihar Legas kwamarade Abiodun Michael ya jinjnawa hukumar akan maida tanancewar na bai daya, wanda yace hakan ya ragewa ‘yan fansho wahala musamman wadanda tsofaffi da sai sun tafiya mai dogon zango don halartar tan-tancewar
Shima Mista Daniel Okoro, Mataimakin Sakatare na kungiyar ‘yan fansho na ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka yi ritaye reshen hihar Legas ya nuna gansuwar sa da tan-tancewar, inda ya ce, ‘yan fanshon sun fito ne kwansu da Kwarkwata sakamakon wayar ma su da kai da kungiyar tasu ta yi.