Kudin Fansho: Maina Ya Maka EFCC A Kotu

Tsohon Jagoran Kwamitin Shugaban Kasa na yiwa Hukumar Fansho Garambawul, Abdulrasheed Maina, yam aka Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu a gaban kotu bisa zargin bata mishi suna.

A wata kara wacce ya shigar  ranar 15 ga watan Janairun 2018, wanda Lauyansa, Mista James Onyilo ya shigar a madadinsa a Babbar Kotun Tarayya dake Lafia, Maina ya zargi Magu da yin tattaunawa da kafafen watsa labarai, wanda a cikinsu ake bata mishi suna, tare da fadin bayanan da ba na gaskiya ba.

A takardar shigar da karar, lauyan Maina ya bukaci kotun da ta yi shelar tattaunawar da Magu yayi a ranar 30 ga watan Nuwambar 2017 da wacce yayi a ranar 14 ga watan Disambar 2017 a matsayin lamari mai cike da bata suna, cin mutunci da kuma rage kimar Maina a idon al’umma.

Sannan kuma ya bukaci kotun da ta tursasawa Magu kan ya janye wadannan kalaman da yayi, tare da wallafa ban hakuri a akalla manyan jaridu uku cikin kwanaki bakwai daga ranar da aka yanke hukuncin. Sannan ya nemi kotun da ta sanya Magu da EFCC su hada hannu su biya Maina diyyar naira bilyan goma saboda bata masa sunan da suka yi.

Lauya Onyilo ya ce “Wanda ake kara na farko (Magu) yana da wani abu a ransa game da Maina. Don haka yake amfani da wanda ake kara na biyu (EFCC) don cin zarafin Maina da kuma musguna masa.”

Lauyan ya ci gaba da cewa “Magu ya yi hira da manema labarai a ranar 30 ga watan Nuwamban shekarar 2017, hirar wadda aka watsa ta a gidajen yada labarai da dama na kasar nan, wanda suka hada da jaridu, rediyoyi, talabijin da kuma kafafen watsa labarai na yanar gizo. Wannan hira da Magu ya yi ta yi tasiri sosai wajen bata wa Maina suna a idon mutane a Nijeriya. Haka kuma a ranar 14 ga watan Disambar 2017, Ibrahim Magi ya sake hira da manema labarai a filin jirgin sama na Abuja in da ya bayyana cewa ‘Muna aiki tukuru don ganin mun kamo wanda ya ci kudin fansho (Maina) wanda ya boye. Ku wadannan mutane, ku kuke kareshi. Amma sai mun kamo shi mun hukunta shi.”

Sai dai kuma babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin mika dukiyar Maina ga gwamnatin tarayya, amma da aka fara bincike masu dukiyar na gaskiya sun bayyana a gaban kotu, in da suka bayyana wa kotu cewa dukiyarsu ce ba ta Maina ba.

 

Exit mobile version