Connect with us

LABARAI

Kungiyar Actionaid Ta Yi Taro Kan Illolin Cin Hanci Da Rashawa

Published

on

Kungiyar Actionaid mai samun tallafin kasa da kasa ta gudanar da taro kan matsala da illolin cin hanci da rashawa Nigeria, inda aka tattauna kan tsananin talauci da yadda aka sake mutane suka shiga cikin talauci saboda balain da matsalar cin hanci da ya addabi mutane ke haifarwa a kasar nan.

Taron an gudanar da shi wannan larabar a Chelsea hotel da ke birnin Abuja, kuma za a kammala ranar jumaa wato kwanaki uku kenan.

Cikin mutanen da suka shirya nazari kan irin matsalolin da nakasassu ke fiskanta musamman akwai shugabannin kingiyoyin kare hakkin dan Adam da na kare hakkin nakasassu da sauran su. Kwamared Musa A. Musa Wanda cikin jawabinsa ya bayyana cewa a kullum yakan tashi da tunani game da yadda za a magance matsalolin cin hanci a kasar nan saboda yawancin abubuwan da ake shiryawa don nakasassu ko marasa galihu bada gudana yadda ake tsara su,  lamarin da  ke nuna akwai bukatar tashi a tsaye don ganin an magance wadannan matsalolin don a samu gina kasa.

Kwamared Umar Ali goro tsohon Kansila kuma shigaban kungiyar nakasassu a jihar Gombe. Shima cikin jawabinsa ya bayyana irin matsalolin da nakasassu ke fiskanta a matsayin abin kaico saboda rashin tausaya musu da gwamnati ko masu rike da madafun iko ke yi. Inda yace mutanen gari suna tausaya musu saboda ya taba tsayawa takarar Kansila ana gani kamar ba zai kai ga nasara ba amma mutane suka zabe shi, kuma Yayi aikin da cikakkun mutane marasa nakasa suka kasa yi. Inda yace ya tona rijiyoyi kusan 200 ya gina asibitoci da makarantu masu yawa.

Don haka ya koka game da yadda cin hanci ke taka rawa a tsakanin jamian gwamnati a duk lokacin da aka ce wani hakki na nakasassu ya fito tsakanin maaikata sai cin hanci ya yi tasiri a  tauye musu. Don haka ya shawarci nakasassun da su tashi a tsaye kan hakkokin su don su ci gaba.

Umar Goro Gombe ya yaba da kokarin kungiyar Actionaid na shirya wannan taro a Abuja da kuma yadda suke shiga yankunan karkara don yin nazarin matsalolin da mutane ke fiskanta musamman wadanda cin hanci da rashawa ke jawowa don a ci gaba da wannan aiki a samu tsarkake kasa daga matsalolin cin hanci da raahawa.

Mista Timothy Ali Yohanna na kungiyar Grassroots research association daga jihar Borno kasancewarsa jamiin da ya kasance cikin wadanda suka gudanar da nazari kan illar da cin hanci ya haifar a tsakanin mutane musamman a jihohin shiyyar Arewa maso gabas ya ce lamarin Yayi muni sosai yadda duk kokarin yakar cin hanci da rashawa da ake yi ba a samun nasarar da ake nema. Don haka ne a kullim talauci ke kara Mamaye mutane ake shan wahala sosai.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: