Daga Ibrahim Muhammad,
Kungiyar masu sana’ar sayar da wayoyin tafi da gidanka na Kasuwar Bata “Bata Global GSM Billage Market” ta sun karrama shugabar reshen Bakin Ja’iz da ke kan titin Tafawa Balewa a jihar Kano.
‘Yan kasuwar wayar na “Bata Global” karkashin jagorancin Shugaban kungiyar Alhaji Ahmad Tijjani Isma’il ya ce, makasudin ziyatar ta godiya ce da karramawa suka ga Shugabar Bankin na Ja’iz Hajiya Na’ima a bisa gamsuwa da suka yi da irin kulawa da ta yi na samarwa ‘yan kungiyar damar cin gajiyar bashi mara ruwa da banking ke baiwa ‘yan kasuwa da masu sana’oi.
Ahmad Tijjani Isma’il ya ce, a kallah ‘yan kungiyarsu ta masu saida waya sama da 100 sun amfana da irin wannan lamuni na kudi da aka basu da yakai na N150,000 kuma hakan ya dada bunkasa sana’ar su.
Shugabar reshen bankin na Ja’iz ta yi wa tawagar jawabi gamsasshe akan wasu al’amura da suka shige musu duhu game da huldarsu da bankin da kuma yanda za su bi matakai don cin gajiyar tsare-tsaren da Gwamnati take na tallafawa sana’oi da bankin ke samun damar gudanarwa in damar hakan ya taso.
Na’ima ta ce, nan gaba kadan bada dadewa za su sake zama da ‘yan kungiyar domin karawa juna sani akan yanda wasu tsare-tsare ke tafiya da yanda yan kasuwa irinsu zasu iya cin gajiya akai.
Cikin ‘yan tawagar da masu saida wayoyin da suka je suka shaidi karramawar kwai shugaban kungiya masu saida wayoyi na jihar Kano da akafi sani da “MOPSA” Ambasada Ibrahim Rabiu Tahir wanda ya nuna jin dadinsa bisa irin goyon bayanda Bankin na Ja’iz ke ba ‘yan kungiyar masu wayoyin domin bunkasa sana’arsu.