Kungiyar EU Ta Horas Da ‘Yan Jarida 50 Hanyoyin Bayar Da Sahihin Rahotannin Zabe A Kebbi

Daga Umar Faruk Birnin Kebbi,

Kungiyar Tarayyar Turai mai goyon bayan mulkin dimokuradiyya a Nijeriya (European Union Support to Democratic Governance in Nigeria ) ta horar da ‘yan jarida sama da 50 a Jihar Kebbi kan rahotannin zabe gabanin zaben qananan hukumomin da za a yi a ranar 5 ga Fabrairu a jihar.

Jami’in kula da ayyukan na ECES, Mista Hamza Fassi- Fihri, ya bayyana haka a lokacin horon da aka yi a Birnin Kebbi a dakin taro na Jamvaly Otel, inda ya ce taron ya kasance na kwanaki uku ne bisa bukatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi (KESIEC).

Ya ce, “Mun yi farin ciki da samun damar kafa wadannan horaswar tare da hadin gwiwar abokan huldar mu na EU-SDGN, Gidauniyar Albino da Asusun Tallafin Mata na Nijeriya.

“Kwarewa ya nuna cewa babu dimokuradiyya ba tare da ‘yan jarida masu ‘yanci ba. Kuma babu wata hukumar mai ‘yanci ba da rahoto ba tare da ‘yan jarida ba.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa yana da mahimmanci a ci gaba da saka hannun jari a kokarin horar da ‘yan jarida, tallafa wa ci gaban sana’ar su da kuma ci gaba da iliminsu na zamani.”

Fassi- Fihri ya bayyana cewa, makasudin gudanar da taron shi ne cimma manufofin da aka sa gaba da kuma ba da damar zurfafa bincike kan yadda za a gudanar da zabe a matsayin muhimmin aikin ‘yan jarida.

“Zabe muhimmin lokaci ne a rayuwar dimokuradiyya, amma yana zuwa da kalubale da yawa, qasada, matsa lamba da kuma wani lokacin ma barazana da tashin hankali.

“Bayar da rahotanni kan batutuwa masu mahimmanci kamar zabe na buƙatar babban matakin ƙwarewa, farawa da cikakken ilimi da fahimtar tsarin zabe.

“Wannan baya ga yin nazari sosai kan yanayin siyasar da za a gudanar a cikinsa.

Ya ce bukatar sanin aikin KESIEC zai taimaka wa ‘yan jarida su fahimci kalubalen da hukumar ke fuskanta domin samun ingantaccen rahoto ga masu sauraro.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa horon zai taimaka wajen kara dankon zumunci tsakanin KESIEC da kafafen yada labarai domin samun ingantacciyar dimokaradiyya ta cikin gida.

Ko’odinetan ya kuma miqa godiyarsa ga kwamishinonin hukumar KESIEC da kuma shugaban KESIEC Alhaji Muhammad Aliyu Mera da sauran masu ruwa da tsaki bisa gayyatar da suka yi wa ECES domin tallafa wa wannan horo da kuma tarbar da aka yi musu

Exit mobile version