Kungiyar Gwamnonin PDP Ta Bukaci Yin Gyara Kan Yadda Ake Gudanar Da Milkin Kasar Nan

Magance Matsalar Tsaro

Daga Idris Aliyu Daudawa

Yayin da ake ci gaba da kasancewa cikin halin rashin tabbas, domin yawan tashe- tashen hankula nau’oi daban-daban a fadin tarayyar Nijeriya, kungiyar gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP, a jiya ne, ta  kira wani taron gaggawa  inda suka zauna, suka kuma ga ya dace da a sake fasalin alkiblar tsarin siyasa,watakila ko su a ganin su, yin hakan zai iya samar da maslaha a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Saboda su a nasu sanin idan ba a dauki matakin yin hakan ba,sai ikon Allah ne kadai zai iya hana wani mummmunan al’amari ya faru.kungiyar ta kara fadakar da cewa kasar tana saurin zama kasa wadda take neman durkushewa a, karkashin jagorancin gwamnatin tarayya ta jam’iyyar (APC).
Gwamnonin PDP sun nuna damuwar su cewa dukkan al’amuran da suka shafi Nijeriya yanzu, abin yana da ban matsoro matuka, musamman ma bambance-bambancen da ke cikin kasar, gwamnatin wadda take kan gado ita ce bar mutane suna yin abubuwan da suka ga dama, gwamnatin tasa ido ne kawai kamar sun fi karfinta ne a  da suka hadacewar su gwamnonin.
Gwamnonin adawar sun bayyana hakan ne a cikin sanarwar da suka fitar a karshen taron nasu, a Makurdi babban birnin jihar Benuwe.
Taron ya samu halartar Gwamnonin sun hada da Aminu Waziri Tambuwal, na Jihar Sakkwato; Okezie Ikpeazu, Jihar Abia; Udom Emmanuel, Jihar Akwa Ibom; Douye Diri, Jihar Bayelsa; Samuel Ortom, mai masaukin bakin na Jihar Benue; Ifeanyi Okowa, Jihar Delta da Ifeanyi Ugwuanyi, Jihar Enugu.

Sauran sun hada da Nyesom Wike, na Jihar Ribas; Oluseyi Abiodun Makinde, Jihar Oyo, Darius Dickson Ishaku, Jihar Taraba; Ahmadu Umaru Fintiri, Jihar Adamawa; Godwin Obaseki, na Jihar Edo da mataimakann gwamnan jihar Bauchi, Baba Tela.
Wadanda suka halarci taron har ila yau sun hada da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus da kuma  shugaban kwamitin amintattu, Sanata Walid Jibrin
kungiyar gwamnonin PDP, a cikin sanarwar, wadda Tambuwal ya sa ma hannu, tunda shi ne shugaban kungiyar ya karanta, ya bayyana cewa kasar tana matukar bukatar gwamnati a matakin ta tashi tsaye “domin kaucewa bala’in da ke tafe muddin ba a dauki mataki ba.”
A cewar gwamnonin, zargin rashin iyawar da gwamnatin APC take jagoranta na gudanar da mulki ya haifar da “rikice-rikicen kabilanci, ga kuma rarrabuwar kawunan al’umma, ta addini, da dai sauran nau’ukan abubuwa mabambanta masu tayar da hankali al’umma.
Daga karshe sun  kara  jaddada cewa yana da matukar ban tsoro cewa “tsaron rayuka mutane yanzu da dukiyoyin su ‘ abin ayan da kamar wuya idan aka yi la’akari da abubuwan tayar da hankali da suke faruwa, a karkashin wannan gwamnatin sakamakon yadda wasu suke  tafiya da nasu  salon jagoranci da rashin iya tafiyar da al’amuran Nijeriya.”

Exit mobile version