Kungiyar Likitoci ta Nijeriya, NARD ta yi barazanar tsunduma yajin aiki idan har ba a sako abokiyar aikinsu, Dokta Popoola Ganiyat kafin ranar 26 ga watan Agusta ba, da aka yi garkuwa da ita.
Shugaban NARD, Dr. Dele Abdullahi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba.
- Likitoci 10,000 Kacal Suka Rage A Nijeriya – NARD
- Gwamnonin Nijeriya Sun Aminta Da Salon Mulkin Tinubu
Dr. Abdullahi ya ce, kungiyar ta daina hakuri da halin ko-in-kula da gwamnati ke nunawa kan sace Dr. Ganiyat.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, an yi garkuwa da Dakta Ganiyat, wacce ma’aikaciya ce a sashin kula da lafiyar ido da ke cibiyar kula da ido ta kasa, Kaduna, a ranar 27 ga watan Disamba, 2023, tare da mijinta da kuma dan ‘yar uwarta.
An saki mijinta a watan Maris, amma Dr. Ganiyat da danta suna tsare a wurin masu garkuwar.