Daga Ahmed Muh’d Danasabe,
A ranar Asabar da ta gabata ne wata kungiyar ci gaban matasa, wato ‘Love Your Neighbour Youths Association’ dake Unguwar Kura a birnin Lokoja ta karrama Shugaban Karamar Hukumar Lokoja, Hon Muhammed Danasabe Muhammed, a bisa gudunmawarsa da kuma jajircewarsa wajen cigaban matasa da kuma mata a karamar hukumar.
Da yake mika lambar yabon ga shugaban karamar hukumar, shugaban kungiyar ta Lobe Your Neighbour, wanda yace mika lambar yabon yana daga cikin bukukuwan cikar kungiyar shekaru biyu da kafuwa, ya kuma bayyana da cewa kungiyar ta karamma Hon Muhammed Danasabe Muhammed ne saboda kudurinsa na kula da rayuwar matasa da kuma mata dake karamar hukumar, da ma jihar Kogi bakidaya.
Kwamred Adamu ya kuma kara da cewa kungiyar su na karamma mutane hazikai ne wadanda suka bada gudunmawarsu wajen ci gaban al’umma.
Hon Danasabe Muhammed yace karrama shi da kungiyar tayi zai kara masa azama da kwarin gwiwar gudanar da ayyukan raya kasa da zasu kyautata rayuwar al’ummar karamar hukumar Lokoja.
Ya kuma ce akwai shirye shirye da gwamnatinsa ke shirin aiwatarwa domin ci gaban matasa da kuma mata dake karamar hukumar, inda har ma ya nemi hadin kan al’ummar karamar hukumar a kokarin data gwamnatinsa keyi na inganta rayuwarsu.
Sai dai kuma ya shawarci matasa dasu guji shiga ayyukan aikata laifufuka irinsu tu’ammali da miyagun kwayoyi da fashi da makami da garkuwa da jama’a da shiga kungoyoyin asiri da dai sauran ayyukan laifufuka makamantarsu, yana mai jaddada cewa karamar hukumar Lokoja karkashin kulawarsa ta kauduri aniyar samar da cikakken tsaro a sassa daban daban na karamar hukumar don dakile ayyukan laifufuka da kuma batagari dake barazana ga sha’anin tsaro a yankin.
Daga nan Hon. Muhammed Danasabe Muhammed ya yabawa kungiyar ta Love Your Neighbour a bisa kafa kungiyar, wadda a cewarsa kungiyar ce da za ta taimaka wa rayuwarsu da kuma kawo cigaba a cikin al’umma, sannan ya yi kira ga sauran matasan da su kafa irin wannan kungiyar don ci gaban matasan.