Kungiyar masu masana’antu ta kasa ta nemi gwamnatin tarayya da na jihohi da su daidaita tare da hada kan dukkan harajin da ake kakaba wa masu kanana da matsaikaitan masanan’atu don rashin yin haka yana zama barazana ga bunkasar masana’antun ne da kokarin samar da aikin yi ga matasa a kasar nan.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ta umarci bankunan kasuwanci su rage kudin ruwa da ake dorawa bashukan da ake karba don bude masana’antu da kuma rage kudin ruwa da farashin kudin musaya na kasashen waje, sun kuma nemi a rage kudin ruwan da aka dora a kan bashin da aka bayar a lokacin annobar cutar korona.
- Takardun Karatun Tinubu Ba Na Bogi Ba Ne – Fadar Shugaban Kasa
- Kungiyar Kasar Sin Ta Lashe Dukkan Lambobin Zinare Na Wasannin Nutso A Gasar Wasannin Kasashen Asiya
Shugaban kungiyar na kasa, Francis Meshioye, da shugaban kungiyar a jihohin Kwara da Kogi, Rahman Bioku, suka yi wannan bayanin a taron su na shekara-shekara karo na 9 da aka yi a garin Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Meshioye ya ce, cikin manyan matsalolin da masu masana’antu ke fuskanta sun hada da yadda ake kakaba musu haraji da kuma lallacewa hanyoyi da wasu kayan more rayuwa da gwamnati ke samarwa.
“Muna fatan gwamnatin Jihar Kwara za ta yi mana maganin wadannan matsalolin don haka zai taimaka muna wajen kara bunkasa harkokinmu a cikin jihar.”
Meshioye, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kungiyar na yankin kudu maso yammacin kasar nan, Kamoru Yusuf, ya ce, tsare-tsaren gwamnati na ‘yan watannin nan, kamar janye tallafin man fetur da kayyade canjin kudaden kasashen waje sun taimaka wajen durkusar da harkokin masu masana’antu a Nijeriya.