Kwamrade Haruna Sale da ya fito daga karamar hukumar Kubau dake a cikin jihar Kaduna ya zamo sabon shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumi reshen jihar NULGE.
Sale zai jagoaranci kungiyar tare da sauran wadanda aka zaba har zuwa tsawon shekaru ana dai zabe Sale ne shugaban a taron kungiyar karo na bakwai da aka gudanar a garin Kaduna.
An kuma gudanar da zaben ne a karkashin kulawar daya daga cikin shugabannin kungiyar ta kasa Kwamarde Razak Lawan.
Sale ya zamo sabon shugaban kungiyar ne bayan da abokin hamayyar sa Kwarade Aliyu Ibrahim wanda ya fito daga karamar hukumar Kaduna ta Kudu ya janye masa.
Da yake tattauna da jadidar Leadership Ayau, Aliyu Ibrahim ya ce, ya janyewa sabon shugaban kungiyar ce saboda irin gudunmawar da ya bayar a baya wajen ciyar da kungiyar da kuma daukacin yayanta gaba, musamman wajen tabbatar da hadin kai a tsakanin yayan kungiyar.
Aliyu Ibrahim ya kuma shawarci sabon shugaban na kungiyar ta NULGE da ya ci gaba da ayyuaka ma su kyau da yake yi don kara daga martabar kungiyar da kuma yayanta, tare da jan daukacin yayan kungiyar ba tare da nuna banbancin addini kona kabiala ba.
A jawabin sa na amincewa da zabar sa sabon shugaban kungiyar Kwarade Haruna Sale ya yi kira ga daukacin yayan kungiar su bashi goyon baya da kuma shawarwari na gari don kai kungiyar ga tudun mun tsira.
Haruna Sale ya baiwa yayan kungiyar tabbacin yin aiki tukuru da kuma jan daukacin yayan kungiyar a jiki don gudanar da ayyukan da zasu samar da ci gaban kungiyar da kuma daukacin yayanta.
A karshe, sabon shugaban ya kuma jinjiwa Gwamnan jihar Kaduna malam Nasir Ahmed el-rufai kan wanzar da biyan sabon albashi mafi karanci ga kananan ma’aikatan dake jihar.