Zubairu T M Lawal" />

Kungiyar NURTW Ta Rantsar Da Sabbin Shugabannin Ta A Nasarawa

Kungiyar masu motocin sufuri ta kasa reshen jihar Nasarawa, ta rantsar da sabbin Shugabannin da yawansu ya kai kimanin ashirin da shida.
Da yake jawabi a madadin Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Sulaiman Abdulkadir Musa ya ce; hakika na wakilci Shugabanmu a wajen rantsar da sabbin Shugabannin wannan kungiyar reshen jihar Nasarawa.
Wadannan sabbin Shugabannin sun kasance ‘ya’yan kungiyar, sun amince masu da su ci gaba da gudanar da mulki ba tare da hamayya ba.
Kuma “Na bi diddigi na tabbatar da amincewar ‘ya’yan kungiyar da suka amince da wadannan da aka rantsar da su ci gaba.
Salisu Adamu, shi ne sabon Shugaban kungiyar wanda ya samu nasarar zarcewa kan kujerar bayan ya shafe shekaru hudu , ‘ya’yan kungiyar suka sake amincewa da ya ci gaba da mulki ba tare da hamayya ba.
Da yake zantawa da manema Labarai bayan rantsar da su, ya ce wannan amincewar da ‘ya’yan kungiyar suka yi masa tare da sauran Shugabannin ba karamin nauyi ba ne. Kuma kalubale ne a gare shi, saboda ayyukan da suka yi a baya wanda ya sanya ‘ya’yan kungiyar suka ji dadi kuma suka amince da mulkin na su.
To yanzu dole su kara kaimi fiye da ayyukan da suka yi a mulkin su na baya.
Sannan ya bukaci ‘ya’yan kungiyar da su kara taimaka masu da addu’a. Da kuma ba su hadin kai wajen gudanar da ayyukan ci gaba.
Sannan ya bukaci ‘ya’yan kungiyar da su kasance masu bin doka da oda da kiyaye tukin ganganci.

Exit mobile version