Hadin gwiwa da kungiyar ‘ONE Germany’ zai bunkasa shigowar masu zuba jari nahiyar Afirika, kungiyar ta bayyana haka ne a takardar sanarwa da aka raba wa manema labarai a kan ziyarar da Shugaban kasa Jamus, Olaf Scholz, ya kawo Nijeriya da Ghana daga ranar Lahadi da ta gabata.
Kungiyar ta yi kira na musamman ga shugaban kasar na Jamus da ya samar da yanayi da zai karfafa ‘yan kasuwar kasar Jamus don su shigo su zuba jari a bangarori daban-daban na tattalin arzikin nahiyar Afirika.
- Yadda Na Sha Mugun Duka A Hannun ‘Yansanda — Ajaero
- Hukumar Alhazai Ta Jihar Kebbi Ta Samu Sabon Shugaba
Daraktan kungiyar ta ‘ONE Germany’, Stephan Edo-Kreischer, ya kara da cewa, “Yadda Shugaba Scholz ya dauki zuba jari a nahiyar Afirka da muhimmancin gaske, abu ne da ya kamata duk dan kasar Jamus ya yaba da matakin, musamman ganin zuba jari a Afirka tamka karfafa tattalin arzikkn kasa Jamus ne, a kan haka bai kamata a bari wannan kokari ya zama furuci na siyasa ba kawai.
“An dade kasashen da suka ci gaba a Turai suna watsi da Afirka, a kan haka wasu kasashe ke komawa wasu kasashe kamar Chana, yanzu lokaci ya yi da za a karfafa danganta da Afirka don gudanar da hulda mai amfanar da juna.
“Wannan kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da Afirika ke tsananin bukatar karin jari don bunkasa bangarorin tattalin arziki da dama. Afirka na bukatar a ji muryarta fiye da duk wani lokaci a baya.”
Daraktan kungiyar a Nijeriya, Stanley Achonu, ya ce shugaban kasar Jamus, Scholz ya jagoranci kiran kara zuba jari a Afirka a kuma shigo da Afirka a cikin manyan kungiyoyin bunkasa tattalin arziki na duniya.
Achonu ya kuma kara da cewa, “Shuugaba Scholz ya jagoranci kiran a tabbatar da shigo ga Afirka a cikin tafiyar kungiyar G20, wanda kuma tuni a aka sanya Afirka a taron da aka gudanar kwanan nan. Amma lallai wannan bai isa ba, dole Afirka ta samu wakilci a manyan cibiyoyin kudi na duniya.