Connect with us

RIGAR 'YANCI

Kungiyar WDDA A Zariya Ta Samar Da Ruwan Sha A Rafin Yashi

Published

on

A farkon makon jiya ne kungiyar ci gaban gundumomin waje a karamar hukumar Zariya, wato Waje District Debelopment Association (WDDA) ta kaddamar da wata na’urar samar da ruwan sha ta zamani ga al’ummar garin Rafin Yashi da suke gundumar Dutsen Abba a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.

Wannan katafaren aiki da wannan kungiya da aka ambayta ta aiwatar a wannan gari na Rafin Yashi, shi ne aiki na biyu da kungiyar ta aiwatar, na farko shi ne na tsayawar da kungiyar ta yi a shekarun da suka gabata, karamar hukumar Zariya suka gina wa al’ummar wannan gari makarantar firamare, wanda kafin ginin makarantar, yaran wannan gari na tafiyar fiye da kilo mita biyar wajen zuwa makarantar firamare.
Tun farko a jawabinsa shugaban kungiyar WDDA Alhaji Garba Salihu Mohammed da farko cewa ya yi, sun yanke shawarar samar da wannan na’urar samar da ruwan sha da sauran bukatu ga al’umma Rafin Yashi da sauran garuruwa da suke tare da wannan gari, bayan sun fahimci matsalar da suke fuskanta shekaru da dama da suka gabata, na rashin rowan sha, kamar yadda jami’in watsa labarai na wannan kungiyar Malam Mutawakilu Yusuf ya shaida ma su.
Alhaji Garba Salihu ya ci gaba da cewar, tun da suka fahimci matsalar al’ummar wannan gari na rashin rowan sha, wanda ya ce sun fahimci, waje guda al’ummar garin suke shan ruwa da dabbobi, wannan, a cewarsa, ba karamar matsala ba ce da ta shafi al’ummar wannan gari, musammama rn bangaren da ya shafi kiwon lafiyarsu.
Wannan matsalar rashin ruwa da al’ummar wannan gari ke fuskanta, a cewar Alhaji Garba Salihu Mohammed, ya sa wannan kungiya ta yunkura na ganin ta warware wa al’ummar wannan gari wannan matsala, ya ce ya na fatan al’ummar wannan gari, za su sa hajjar mujiya day a shafi tsaron na’urorin da aka sad a za su samar da rowan da ake bukata.
Shi ko Shattiman Tudun Wadan Zariya, kuma masanin ilimi, Alhaji Aliyu Sabo, kira ya yi ga al’ummar wannan gari na lallai ne su kara motsawa na ganin sun a sa yaransu maza da kuma mata makaranta, domin su sami wadanda za su share ma su hawaye a nan gaba.
Alhaji Aliyu Sabo, ya kuma nuna matukar damuwarsa ga yadda ‘yan siyasa ke juya wa al’umma baya, bayan zabe, kamar yadda ya ce, lokaci ya yi da al’umma, ba al’ummar Rafin Yashi kawai ba, za su rika shiga siyasa, ta yadda za a sami wakilai nagari kuma ma su amanar da za su rika juya baya ga al’ummar da suka zabe su, na ganin sun cika ma su alkawarin da su ka yi ma su kafin zabe.
A dai lokacin wannan taro, fitaccen malamin Jami’an nan da ke koyarwa a Jami’ar tunawa da Tafawa balewa da ke Bauchi, Malam Mukhatar Adamu dandajeh, nuna damuwarsa ya yin a yadda zababbu ke aiwatar da ribar dimukuradiyya ga al’ummar da suka zabe su, a cewarsa, rarraba abubuwan hawa ko biya wa talaka kudin zuwa aikin hajji da dai rabon ribar dimukuradiyya da wasu ‘yan siyasa ke yi, duk, kamar yadda ya ce, lokaci ya yi da za su canza salon rabon, ta mayar da hankalinsu wajen tallafga wag a bangaren ilimi da kiwon lafiya da samar da kyakkywan rowan shad a kuma samar da hasken wutar lantarki da kuma samar da hanyoyin da al’ummar karkara za su bi, kamar yadda al’ummar da su ke birane ke bi.
Alhaji Mansir Yahaya, ya nuna matukar jin dadin al’ummar Rafin Yashi ga wa shugabannin wannan kungiya ta WDDA, na yadda ta mayar da garinsu ‘yar lele, musamman, a cewarsa, bayan kungiyar ta tsaya ansamar da makarantar firamare sai kuma samar ma su da rowan shad a suka yi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: