Al’ummar yankin unguwar Rimi da ke yankin karamar hukumar Kumbotso sun bayyana mutukar jin dadinsu bisa dauki da hadaddiyar kungiyar ’Yan tifa na Jihar Kano su na kawo mu su na samar da kasa, domin cike hanyar dan saukaka mu su wahalar rashin.kyawun hanyar da su ka jima a ciki.
Hanyar ta Unguwar Rimi da ta dade a lalace har ta kai da damina ba ta saukin yiyuwa hakan ta sa Kungiyar ’Yantifa karkashin jagorancin Kwamred Mamunu Ibrahim Takai samar da kasa da a ka gudanar cike da dandabe hanyar.
Da mu ka tuntube shi a kan dalilin gudanar da aiki Shugaban Hadaddiyar Kungiyar ta ’Yantifa na Jahar Kano ya ce, akalla hanyar da ta kai kilomita biyu da rabi, don haka su ka ga ya dace su gyara duba da su na su na da alaka da hanyar, domin motocinsu na bin ta su je debo kasa wannan kuma gyaran kyautata a takace tsakaninsu da al’ummar yankin.
Shugaban na ’Yantifa na Jahar Kano ya ce, aikin hanyar ya ci tifar kasa kusan 100, inda wannan kuma su ka samo gireda ta dandabe a ka kuma bi da motar ruwa.
Mamunu ya ce, akwai dai dai-daikun mutane da su ka ba su gudunmuwa akwai wanda shi ne ya samar da gireda da a ka dandabe kasar, sannan kuma akwai wani bawan Allah mai kamfanin kwangila da ta sa a ka kawo motar ruwa a yayin aikin.
Kwamred Mamuna Ibrahim Takai ya ce, akwai kungiyar cigaban al’ummar Unguwar da su ka jinjina mu su a kan aikin wanda zai mutukar rage mu su wahala da su ka dace a ciki. Ya kuma jaddada cewa, kungiyar tasu ta ’Yantifa a shirye ta ke wajen bada gudunmuwa da zai taimaka wa cigaban al’umma a kowane yanayi na saukaka rayuwa.