ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kungiyoyi Da Abokan Arziki Na Ci Gaba Da Taya Dantsoho Murna

by Bello Hamza and Sulaiman
4 months ago
Dantsoho

Kungiyoyi da kuma sauran abokan arziki, ba ci gaba data taya Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA Dakta Abubakar Dantsoho bisa zama Mataimakin Shugaban Kungiyar Tashoshin Jiragen Ruwa ta duniya wato IAPH.

Daya daga cikin su ita ce, Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Kasa  wato NSC wadda Sakatarenta kuma shugabanta Dakta Akutah Pius Ukeyima, ya bayyana cewa, zabar Dantsoho a mukamin hakan ya nuna salon shugabancinsa, na tafiyar da Hukumar ta NPA, musamman yadda ya mayar da hankali, wajen kara bunkasa fannin na sufurin kasar.

“Wannan nasarar da  Dantsoho ya samu babban abin alfahari ne, ga kasar nan wanda kuma hakan ya nuna irin shugabanci na gari na Dantsoho ke ci gaba da yi ne, a bangaren Hukumar da kuma a bangren ruwa,” Inji Dakta Akutah.

ADVERTISEMENT

Kazalika, Hukumar ta kuma jinjinawa Dakta Dantsoho kan samar da dabarun tsare-tsaren da suka kara saita fannin sufuri a kasar da kuma a fadin duniya.

Ya bayyana kwarin guiwarsa da cewa, shugabancin na Dantsoho, ya taimaka matuka wajen samar da damarmaki da dama a nahiyar Afirka, wanda hakan ya kuma kai Nijeriya ga wani babban mataki a bangaren sufurin Jiragen Ruwa a Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Danyen Mai Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.436 —OPEC

An Jinjina Wa Tinubu Bisa Mayar Da Ofishin Ayyukan NPA Garin Warri

Ya kuma sanar da ci gaba da bai wa shugabancin Dakta Dantsoho goyon baya, musaman domin kara samar da sauye-sauyen da za su kara bunkasa hada-hadar zirga-zirga, da kuma a bangaren kara bunkasa kasuwancin tatalin azrki na Teku.

A nan kuma Kamfanin Rukunonin SIFAD, ya taya Dakta Dantsoho murnar zama Mataimakin Shugaban na kungiyar ta IAPH.

Hakan na kunshe ne, a cikin wata wasika da Shugaban Kamfanin Dakta Taiwo Afolabi CON ya fitar ta taya murnar, inda ya danganta zabar Dantsoho kan mukamanin a matsyin abinda ya dace, musamman duba irin salon shugabanci na gari na Dakta Dantsoho, wanda hakan ya sanya ya samar da gagarumar gudunmawa a bangaren sufurin Jiragen Ruwa na kasar.

Shugaban sashen samar da bayanai na Kamfanin  Mista Olumuyiwa Akande, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

“Wannan zaben na ka ya nuna irin kwarewar da kake da ita da kuma shekarun da ka shafe, kana yiwa Hukumar aiki wadda ta faro tun daga lokacin da ka yi aikin yiwa kasa hidima a Hukumar a shekarar 1992, inda a yanzu kuma ka kasance shugaban Hukumar ta NPA, “ A cewar Afolabi.

Ya kara da cewa, iya salon shugabanci na gari da kuma sauye-sayen da Dakta Dantsoho ya samar a hukumar, sun kara karfafa ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.

A cewarsa, nasarorin da shugaban ya samar a Hukumar ba wai Hukumar ce kadai za ta amfana ba, har da daukacin fadin nahiyar Afirka

Kamfanin ya kuma bayyana kwarin airin Dakta Dantsoho zai yi amfani da sabbin dabarunsa na kara karfafa hadaka domin kai Afirka .

“Kamfanin na alfahari da nasarorin da ka samar da kuma ci gaba da kara ciyar da Hukumar gaba,”Inji Afolabi.

Kazalika, Kamfanin na SIFAD ya kuma kara jaddda goyon bayansa kan shiye-shiryen da Hukumar ke ci gaba da yin a kara ciyar da Hukumar gaba

Ya kuma ayyana ci gaba da yin hadaka da Hukumar ta NPA, musamman domin kara fadada gasa a bangaren sufurin Jiragen Ruwa na kasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Danyen Mai Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.436 —OPEC
Tattalin Arziki

Danyen Mai Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.436 —OPEC

December 19, 2025
An Jinjina Wa Tinubu Bisa Mayar Da Ofishin Ayyukan NPA Garin Warri
Tattalin Arziki

An Jinjina Wa Tinubu Bisa Mayar Da Ofishin Ayyukan NPA Garin Warri

December 19, 2025
Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
Tattalin Arziki

Gwamna Radda Ya Dora Harsashin Gina Ma’aikatar Sarrafa Rogo A Katsina

December 13, 2025
Next Post
Zulum Ya Ba Da Tallafin ₦300,000 Ga Iyaye, Da Ciyar Da Ɗalibai 90 Kyauta A Borno

Zulum Ya Ba Da Tallafin ₦300,000 Ga Iyaye, Da Ciyar Da Ɗalibai 90 Kyauta A Borno

LABARAI MASU NASABA

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.