• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kungiyoyi Masu Fada Aji Kan Harkar Ilimi Sun Nemi A Yi Wa Sashen Kwaskwarima

by Idris Aliyu Daudawa
2 months ago
Ilimi

Yayin da ake ta nuna damuwa kwari da gaske kan lalacewar lamarin bangaren ilimi,wadanda suka fi ruwa da tsaki kan lamarin ilimi sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda lamarin ilimi yake ta kara lalacewa magudin jarabawa,sakamakon jarabawa mara kyau a jarabawar cikin gida,da kuma yadda ake kallon abin daga waje, inda suika ce akwai matukar bukatar a dauki tsattsauran mataki.

Kungiyar Malaman makaranta ta kasa (NUT)reshen Jihar Ogun ta yi kira ne,ta bukaci da ayi gyaran da zai shafi kowane bangare na ilimi a kasa baki daya, domin a samu yin gyaran kayan da ake amfani dasu wajen koyarwa,ta haka a nasu ganin,matsalolin da suke da nasabar yadda aka kasa tabuka wani abin kirki lokacin jarabawar, yayin da ita kuma kungiyar Iyayen yara da Malaman makarantu ta kasa (NAPTAN) tana bukatar da,a dawo da, tsarin yadda za’a ja hankalin dalibai ga maida hankalinsu komawa al’adarnan ta karatu,da kuma inganta horon Malamai.

  • Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu
  • Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa

Ita ma a nata bayanin kungiyar dalibai ta kasa ita ma ta nuna kyamar al’amarin gaba daya (NANS)akan abinda ta kira. irin faduwar jarabawar da aka yi a matsayin wata gazawa ce ta yadda ake gudanar da jarabawar.

Nuna rashiun jin dadin nasu ya biyo bayan da hukumar shirya jarabawar ta Afirka ta yamma ta fitar da sakamakon jarabawar na daliban shekarar 2025, wadanda suka kammala karatunsu na Sakandare (WASSCE),abin ko da bayan da ita hukumar (WAEC) ta sake sakin wani sakamakon bayan lurar da aka yi akwai kurakurai na yadda rubuta sakamakon da ba shi ne ya dace ba.

Kungiyar Malaman makaranta ta Nijeriya,reshen Jihar Ogun,ta hannun Sakatarenta na Jahar, Komrade Oyelere Samson,cewa yayi duk da yake tun farko WAEC ta bada sanarwar kashi 87.24 ne na daliban da suka rubuta jarabawar suka samu nasara a darussa biyar ko fiye da haka,sun kuma samu nasarar ce, a darussan da suke da wuyar samu ake kuma mataukara bukatar a samu nasara kansu kamar Turanci da Lissafi, wannan kashi 38.32 ne.

LABARAI MASU NASABA

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Duk da yake hukumar tayi gyara bayan kuskuren da, aka gano saboda tangardar na’ura abin ya koma kashi 91.14, Samson ya tsaya kai da fata cewar,akwai bukatar ayi abubuwa da yawa domin a kara yadda lamarin yake tafiya.

Yawa dalibai da yawa sun dawo daga rakiyar lamarin daya shafi karatu,domin kuwa kafofin sadarwa na zamani sune ke lalata abubuwan da aka saba da su na gaskiya da gaskiya.

“Duk lokacin da muke maganar samun sakamako wanda bai da kyau duk masu ruwa da tsaki dole ace suna da laifi.

“Wadansu na cewa yanzu ilimi ya zama wani abu ne wanda ya zama tamkar wani siddabaru ne,abinda bai kamata bane. Iyaye suma suna da irin gudunmawar da suke badawa dangane da hakan; har akwai wadansu Iyayen da suke zuwa makaranta domin su ci mutuncin Malamai/ Malamai, abinda ba’a taba ji ba shekarun da suka wuce na baya kamar yadda ya jaddada,”.

Bugu da kari har mahanyoyin da ake amfani da su Samson yace da akwai matsala,da yaya za’a ci gaba da amfani da Alli da kuma Bango ko Allon da ake rubutu kan shi, yayin da wasu kasashe suna zuba jarinsu wajen amfani hanyoyin koyarwa na zamani a azuzuwa,da dai sauransu.

Akwai ma maganar kayan more rayuwa wadanda basu da nagarta,yadda ba a karfafawa Malami gwiwa, rashin kwarewa kan darasin da ake koyarwa, irin wadannan abubuwan sune ke bada gydunmawa wajen samun sakamakon da bai da wani amfani.

“Ta yaya kake tsammanin wanda aka koya mashi ko karanci Turanci ace shi ne yake koyar da Social Studies wato darasin da ake koya yadda rayuwar Dan’ Adam take, ko kuma wanda ya karanta Social Studies ace yana koyar da darasin Biology?” ai abin yana da kamar wuya.

Kan hanyoyin da za abi domin maganin matsalolin, Samson ya yi kira da dalibai, Iyaye, gwamnati, da kuma sukwararru “ ad su samar da wani sabon babi na koyarwa da koyo”.Suma hukumomin jarabawa akwai bukatar su dauki tsauraran matakai na hana magudin jarabawar.

Ya kara jaddada cewa, “dukkan masu ruwa da tsaki, farawa daga dalibai kansu, saboda yawancinsu basu nuna sha’awar suna son su koya.

Bullowar kafafen sadarwa na zamani suma suna da tasu illar wajen daukar lokacin dalibai. Abubuwan nda suke kallo ta kafafen sadarwa na zamani duk sun bata wasu abubuwan da za su sa su kasance masu nagarta, sun canza masu zuciyarsu daga koyon wani abu, saboda ywancinsu suna cewa ko iya cewa shi ilimi garesu ba wani abinda suka dauka da muhimmanci bane, abinda kusan baida ko bai kamata hakan ba, ta fito daga bakinsu ba.

“Dalibai su da Iyayensu suma suna da laifi saboda Iyaye ba su yin abubuwan da suka kamata su yi. Saboda yanzu akwai iyayen da suke makaranta ba domin komai ba sai saboda su ci mutuncin Malamin makaranta.

“Duk wadannan abubuwan,babu wanda ya taba jinsu. Don haka dole ne aga laifin su Iyaye tare da masu aikin, domin kuwa muna yiwa lamurran rikon sakainar kashi, yayin da abubuwa suna lalacewa.

“Mutane na maganar yadda ake koyarwa ta zamani a cikin azuzuwa.Mu har yanzu muna amfani ne da da Alli da Allo. Yawancin al’amuran koyarwa,da koyo har yanzu ana yin abin a rubuce ne,ba ayi abin a bayyane bam wato abinda su dalibai za su gani.

“Duk irn wadannan abubuwan suna iya shafar koyarwa da koyo.Ya kuma maganar yadda abubuwan da zasu inganta lamarin koyarwa a makarantunmu,irinyanayin da ake koyarwa da kuma yadda za’a karfafawa Malami gwiwa? Don haka shi ko su Malaman da ba basu kwarin gwiwa, babu wani abubuwan da za su inganta koyarwa da koyo da za su iya yi.Babu isassun Malamai a makarantunmu, Malaman da suka karanta Turanci ana cewa su je su koyar da lamarin da ya shafi mutum da yadda rayuwarsa ta ke.

“Yayin da kuma Malamai wadanda suka karanta social studies,ana cewar su je su koyar da darasin daya shafi kimiyya wato Biology.A irin hali wa ake tsammanin yafi dacewa a ga laifinsa? Don haka duk masu ruwa da tsaki sun taimakawa jagulewar lamarin.Sai abu na uku wacce irin shawara ya dace, aba makarantu, Iyaye, da kuma gwamnati, da su kansu daliban a gaba? Dukkan masu ruwa da tsaki suma su bude wani sabon babi.

“Kamata ya yi mu yi tunani kan abubuwan da suka kamata ayi masu nagarta a Nijeriya.Ya dace ita hukumar Jarabawar ta koyi yadda zata iya maganin wani lamari idan ya tasa,ya kasance kuma yadda za ayi magani wani abu idan ya taso,a dukkan wasu kafafe na jarabawa.Ba zamu iya dora masu wasu abubuwan da suka taso da ake magana kansu,ba daga wurinsu bane maganar gaskiya kamar yadda ya ce,’.

Sai dai kuma,NAPTAN tayi kira da gwamnati da ta bunkasa yadda dalibai zasu so yin karatu har su yi na’am da shi, su gane lalle wata hanya ce ake son taimakonsu, su inganta lamarin horon Malaman makaranta, su zuba jari a bangaren lamarin daya shafi bunkasa aikin,da fasahar kafar sadarwa ta zamani wajen samar da duk abubuwan da suka da ce domin yin hakan, saboda ta haka ne kawai za a iya tafiya daidai da zamani kan lamarin daya shafi ilimi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
ASUU
Ilimi

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Next Post
Dambarwar 2027 Da Kalubalen Da Ke Gaban Jam’iyyun Siyasa

Dambarwar 2027 Da Kalubalen Da Ke Gaban Jam'iyyun Siyasa

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.