Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Kura-kuren Da Hukumomi Ke Yi Wajen Bayar Da Rance

by
1 year ago
in MAKALAR YAU
6 min read
Zamani
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daga Aliyu M. Kurfi (PhD),

Ya kamata mu sani cewa akwai wasu kura-kurai da hukumomi ke yi wajen bayar da rance, wadanda ke jawo durkushewar sana’oi a jihohinmu. Ga wasu daga ciki kamar haka:

  • Rubdugu A Kan Sana’o’i Masu Sauki: Abu na farko dai shi ne saboda karancin jari masu karbar rance kan yi wa sana’oi masu saukin yi rubdugu. Babban dalilin haka kuwa shi ne karamin jari da akan bayar ga masu bukata. Saninmu ne cewa kudaden rance da hukuma ke bayarwa ba su wadata, har a iya yin babbar sana’a da su. Saboda haka wadanda suka karbi irin wadannan kudade domin jari su kan nemi karamar sana’a mai saukin yi, wadda ta gama gari. Su kuwa irin wadannan kananan sana’oi ga sunan lungu da sako na garuruwanmu, wadanda kusan mu ce kasuwarsu cunkushe take. Misali, duk sana’ar da za a yi, idan an samu rance na ‘yan kudade, bisa al’ada, ba ta wuce ta kafinta ba, ko a bude shagon Kwamfuta da wurin daukar hoto, ko shagon dinki da aski, ko sayar da abinci ba. Irin wadannan sana’oi kuwa ga su nan bila adadin a garuruwanmu. 18 Mai karatu, misali ko a hedikwatar karamar hukumarku idan a ka bincika shin masu aski, ko shagunan Kwamfuta, ko na walda da na daukar hoto da gidajen sayar da abinci, da sauransu, ai sunan nan bir-jik, wasu ma babu kasuwa, sai dai akan yi sune domin a samu rufin asiri da kuma magance zaman gida, ga magindanta. To mu kaddara gwamnati ta bayar da rance, wanda hakan ya jawo aka kara bude shagunan sana’oi irin wadannan, da suka gama gari, shin ba mu tsammani cewa daga karshe za a yi mutuwar kasko, a inda da tsofaffi da sababbin sana’oin da yawansu za su durkushe, a cinye jari?
  • Rashin Cika Alkawari: Sauran matsalolin da kan kawo cikas kuwa wasu duk mun san su, watau kamar na dadaddiyar halayyar nan ta masu karbar bashi ta rashin cika alkawari da rikon amana.
  • Rashin Kishin Jami’ai: Akwai kuma rashin kishi nasu kansu jami’an da gwamnatin kan sanya gaba su raba bashi.
  • Bayar Da Bashi Kara-Zube: Sauran matsalolin kuwa su ne wadanda suka danganci bayar da bashi da ake yi kara-zube, a inda wasu lokuttan ma layi a kan yi a na raba bashin ga masu bukata, kamar ana raba abincin sadaka. Bayar da bashi ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba kan jawo gwamnati ta yi asarar kudaden.
  • Bayar Da Kadara Bashi A Matsayin Kudade: Akwai wata matsala wadda ita ce ta rabawa mabukata kayan sana’a maimakon kudade, a inda akan sawo kaya masu tsada a raba a matsayin bashi, wanda kan jawo a yi ba uwar ba ribar, saboda kuwa daga karshe wadanda suka karbi bashin, bisa ga dalilan da muka ambata a baya, su kan sayar da kayan arha, su watsar da sana’oin.
  • Yin Sana’oi Gama-Gari: Har wayau dai wata matsalar ita ce barin wadanda suka amfana da bashin su yi duk irin sana’ar da suke so, ba tare da an sanya su a kan hanya ba. Barin a yi sana’oi kara-zube babu kaidi, kan jawo a yi wa sana’oi na gamagari, masu saukin yi, likimo, wanda kan haifar da cunkushewar kasuwa. A baya dai mun bayar da misalan irin wadannan sana’oi.
  • Rashin Samar Da Kariya: Baya ga haka, wata babbar matsala ita ce ta bayar da bashi ba tare da wata kariya mai inganci ba, da za ta tilasta wanda ya amfana da rancen ya yi hattara dangane da kudaden.
  • Karkatar Da Kudade: Daga karshe ita kanta hukuma da nata laifin saboda kuwa wasu kudaden da ake turowa domin bayar da rance ga marasa karfi, akan zagaye da su a yi wasu ayyukan na dabam; misali a nan shi ne kudaden ‘Sure-P’, wadanda har zuwa yau ba a san inda wasu daga cikin kudaden suka shiga ba a wasu 19 jihohi, sai faman shari’u wadanda basu karewa. Kai da dai sauran matsaloli iri dabam-daban da suka dabaibaye shirin. Shi wannan tsari da muke tallatawa, wanda kasidarnan ke dauke da shi, kafin mu samar da shi an yi la’akari da irin wadannan matsaloli da muka bayyana. Tun a shekarar 2015, watau ‘yan watanni kadan bayan da aka rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari, muka aikawa gwamnatin tarayyya da wasikarmu, mai dauke da wannan mafita ta ‘Certificate For Loan’ ko ‘KWALI JARI’, tare da sauran shawarwari.

 

Labarai Masu Nasaba

Zamanantar Da Tattalin Arziki: Alfanun Kasuwar Baje Kolin Fasaha Da Kawance Tsakanin Nijeriya Da Saudiyya

“Hattara Dai Masu Neman Siyasantar Da Sha’anin Tsaro A Nijeriya”

Tsarin ‘Kwali Jari’

Wannan babi zai yi bita ne a kan wasu daga cikin abubuwan da wasikarmu dangane da KWALI JARI zuwa ga gwamnatin tarayya ta kunsa. Sai dai yana da kyau tun kafin a yi nisa mu sanar da maikaratu cewa abin da zai karanta dan tsakure ne daga wasikar, amma ba dukkanta ba, kuma a cikin harshen Turanci muka rubuta ta. Fatarmu dai ita ce, a fahimci cewa abin da za a karanta a babin ba dukkan abubuwan da wasikar tamu ta kumsa ba ne. Kafin dai mu aika wa gwamnatin tarayya wannan shawara tamu sai da muka gabatar da ita a kafafen sadarwa, wadanda suka hada da gidajen rediyo, da kafafen sadarwa na zamani, watau na yanar gizo, kai har tarukan jama’a mun kira, domin a tattauna wannan tsarin a wasu daga cikin jihohinmu na Arewa-maso-Yamma, wadanda suka hada da Katsina da Kaduna da Kano da Zamfara da Jigawa. Lokacin wannan zagaye namu na tuntuba, mun samu rakiyar wasu daga cikin ‘yan Kungiyar Muryar Talaka.

Mun amfana matuka daga shawarwarin da jama’a suka bayar. Yanzu ga wasu daga cikin batutuwan da muka ciro daga wasikar tamu ga gwamnati, dangane da tsari na KWALI JARI. Bismillah! ….

Wannan tsari da muka gabatar a nan, mun lakaba masa suna KWALI JARI. Babban abin da ake bukata a tsarin shi ne samar wa matasanmu rancen kudade domin su yi sana’a, ta hanyar karbar takardunsu na shaidar kammala babbar makaranta, a matsayin jingina.

ADVERTISEMENT

 A yau, saboda rashin aikin yi wasu daga cikin matasan namu sun kasance ‘yan ta’adda, masu yin garkuwa da mutane, da kuma aikata sauran miyagun dabi’u. Muna da tabbacin cewa za a iya dawo da kimar takardun shaidar ilimi na kammala manyan makarantu ta hanyar yin amfani da wadannan takardu a matsayin jingina, domin bayar da rancen kudade ga matasanmu su yi jari. Saboda haka muna bayar da shawara a amince domin yin amfani da takardun shaidar kammala manyan makarantu, a madadin takardun mallakar fili ko gida wajen bayar da rance. A fili take cewa wannan lokaci da muke ciki, akwai matasanmu wadanda suka kammalla manyan makarantun jibge a birane da garuruwanmu, da a yau suke zaune ba tare da sanin me za su yi ba. Baya ga irin wadannan matasa da ke zaune babu abin yi, duk shekara kuma ana yaye dubbai daga manyan makarantunmu. 21 Sanin kowane cewa hanyoyin da aka dade ana bi wajen samawa matasa sana’oi, hanyoyine na wucin-gadi, wadanda ba masu dorewa ko tasirin kirki ba. Daya daga cikin irin wadannan hanyoyi shi ne Sure-P, da gwamnatin da ta shude ta samar, wanda kuwa mun sani ko a wancen lokacin kalilan ne daga matasan namu masu takardun shaidar kamalla manyan makarantu suka amfana da shi.

Manufar wannan tsari namu na KWALI JARI, shi ne ya taimaka wajen samarwa matasanmu rance kudade domin yin jari, ta hanyar karbar takardunsu na shaidar kammala manyan makarantu da na yin hidimar kasa a matsayin jingina. Mun fahimci cewa ita kanta gwamnati da bankuna za su iya taimakawa wajen magance wannan matsala. Hujjarmu ta Neman a yi Amfani da Wannan Tsari

  • Mun lura cewa yawan dalibai wadanda ke kammala manyan makarantu, duk shekara karuwa ya ke yi, ga shi kuma akwai irin wadannan matasa da suka kammala manyan makarantu jibge ba tare da aikin yi ba.
  • Rashin aikin yi ya yi kamari a wannan kasa, alamar haka kuwa ita ce a duk lokacin da ake neman mutum 10 domin a daukesu aiki, za ka taras mutane1000 sun nuna bukatarsu; haka idan 10,000 a ke nema, a nan za a samu a kalla mutane 100,000 da za su nuna bukatarsu. Idan masu karatu za su iya tunawa ai ba da dadewa ba wasu matasa masu neman aiki a karkashin Hukumar Shige da Fice ta Kasa, watau ‘Nigerian Immigration Serbice’, suka rasa rayukansu wajen turereniya, domin neman aiki.
  • Mun fahinci cewa bankuna suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen magance matsalarmu ta rashin aikin yi, domin habaka ci gaban kasa.
  • Mun gaza fahimtar dalilan da suka sanya takardun mallakar filaye ko gidaje suka kasance sun fi takardun shaidar kammalla babbar makaranta daraja a idon bankuna, wajen bayar da rance. Abun damuwa dangane da matsalar shi ne, a cikin wadannan masu takardun shaidar kammala manyan makarantu har da masu babban digiri. Babban abun takaici dangane da wasu daga cikin irin wadannan matasa masu manyan digirori kuwa shi ne, sun yi wannan karatu ne saboda ganin rashin tasirin digirinsu na farko dangane da samun aiki. Ga wasunsu kuwa a iya cewa ganin hadari ne ya sanya suka yi wanka da kashi, domin kuwa sun yi kuru ne suka kashe ‘yan kudaden da ke hannunsu, da niyyar zurfafa iliminsu, wanda ga zatonsu zai fi taimaka masu wajen saurin samun aikin yi. Sai dai har zuwa yau akwai wasu daga cikin irin wadannan matasa suna nan suna ta gararamba.
  • Haka kuma sanin kowa ne dai, kafin kowane matashi ya samu takardun shaida daga babbar makaranta sai iyayensa sun yi dawainiya da shi ta hanyar kashe makudan kudade a kansa, tun daga makarantar Firamari har zuwa babbar makaranta. Bisa ga haka, har idan dai saboda kima ce wadda ta danganci irin yawan kudaden da aka kashe kafin mallakar wani abu, to mu sani cewa ita ma takardar shaidar kammala babbar makaranta tana da irin wannan kimar. Fatarmu dai anan ita ce kar masu bayar da rance su samu damuwa, domin kuwa gwamnati sai ta goyi bayan matasa masu bukata kamin a bayar da rancen.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Alhakin Shiga Tsakanin ’Yan Kannywood Da Afaka Ya Rataya A Wuyan Ganduje

Next Post

Ya Kone Gidansa Kurmus Don Ya Hana tsohuwar Matarsa Dawowa A Kaduna

Labarai Masu Nasaba

Saudiyya

Zamanantar Da Tattalin Arziki: Alfanun Kasuwar Baje Kolin Fasaha Da Kawance Tsakanin Nijeriya Da Saudiyya

by
3 months ago
0

...

Tsaro A Nijeriya

“Hattara Dai Masu Neman Siyasantar Da Sha’anin Tsaro A Nijeriya”

by
5 months ago
0

...

Koyon Sana’o’i A Matsayin Ginshikin Masana’antu

Koyon Sana’o’i A Matsayin Ginshikin Masana’antu

by
7 months ago
0

...

Gambu

Marigayi Gambu Me Wakar Barayi A Mahangar Kimiyyar Zamantakewa ‘SOCIOLOGY’

by
7 months ago
0

...

Next Post

Ya Kone Gidansa Kurmus Don Ya Hana tsohuwar Matarsa Dawowa A Kaduna

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: