Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya, IPMAN ta kulla yarjejeniya da matatar man Dangote domin dakon man fetur kai tsaye zuwa ga gidajen man kungiyar.
Shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Garima, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, jim bayan wani taron kwamitin ayyuka na kungiyar na kasa.
- Taron Ƙasashen Musulunci A Saudiya: Tinubu Ya Nemi A Kawo Ƙarshen Ta’addancin Isra’ila A Gaza
- Robert Fico: Yin Fito-Na-Fito A Tsakanin Sojojin Rasha Da Ukraine Ba Shi Da Ma’ana
Ya ce, haɗin gwiwar zai tabbatar da samar da man fetur mai saukin farashi a duk faɗin Nijeriya.
“Bayan mun gana da Aliko Dangote da tawagarsa a Legas, muna farin cikin sanar da cewa, matatar Dangote ta amince ta bai wa IPMAN man fetur, Dizal da Kananzir kai tsaye zuwa gidajen manmu.”
Garima ya bukaci ‘yan kungiyar IPMAN da su marawa matatar Dangote baya, inda ya bayyana alfanun cewa, hakan zai habaka tattalin arzikin Nijeriya.