• English
  • Business News
Sunday, October 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwamishinan Kasafin Kudin Jihar Zamfara Ya Bar APC Ya Koma PDP

by Bello Hamza
3 years ago
Zamfara

Kwamishinan kasafin kudi a Zamfara ya saki tafiyar APC, ya kama jam’iyyar PDP mai adawa gabanin zaben 2023.

Alhaji Aliyu ya bayyana cewa, ba zai ci gaba da zama a jam’iyyar da gazawarta ta fi nasararta yawa ba, tuni dan takarar gwamnan jihar Zamfara a PDP ya karbi kwamishinan tare da bayyana kwarin gwiwa a zaben bana.

  • PDP Ta Kori Nnamani, Ogbu, Dan Fayose, Da Wasu Daga Jam’iyyar
  • Mataimakin Gwamnan Sakkwato, Dan Iya, Ya Musanta Ficewa Daga PDP

Sabon rikici na kunno kai a jam’iyyar APC a jihar Zamfara yayin da kwamishinan gwamna Muhammad Bello Matawalle ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Kwamishinan kasafin kudi da tattalin arziki, Alhaji Aliyu Tukur E.S Mafara a wani taron ‘yan jarida a Gasau a ranar Juma’a ya ce ya bar jam’iyyar APC tare da komawa PDP; ya marawa dan takarar gwamnan PDP a jihar, Dauda Lawal.

Alhaji Mafara na daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Zamfara kuma yana daga cikin masu fada a ji a siyasar jihar, LEADERSHIP ta ruwaito.

LABARAI MASU NASABA

Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi

Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Da yake magana bayan ganawa da dan takarar gwamnan na PDP, tsohon kwamishinan ya jaddada cewa, ba zai bari ya ci gaba da zama a inda abu ya ki gaba ya ki baya ba.

A cewarsa: “Na sanar da gwamnatin jihar, tsohon gwamna da kuma mabiya bayana gabanin sauya sheka daga APC zuwa PDP.

“Ina yin wannan ne saboda mutane na, kuma ina da yakini kan Dr. Dauda Lawal, idan aka ba shi dama ya zama gwamnan Zamfara a zabe mai zuwa, zai shawo kan matsalolin tsaro, ya habaka harkar noma, ya samar da kasuwanni masu kyau ga manoma.

“Saboda haka, na ba da dukkan goyon baya na ga jam’iyyar PDP, kuma ina son yin kira ga magoya bayana a Zamfara da su bi tafiyar Dauda Lawal da PDP a zabe mai zuwa.”

Dan takarar gwamnan PDP ya magantu A nasa bangaren, dan takarar gwamnan jihar Zamfara na PDP, Dauda Lawal, ya tabbatar da cewa, Zamfara jiha ce ta PDP, inda ya kara da cewa, jam’iyyar za ta sake samun nasarar karbe mulki a zaben 2023.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi
Siyasa

Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi

October 11, 2025
Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Manyan Labarai

Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

October 11, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Next Post
Gakpo Ya Yi Gaggawar Koma Wa Liverpool, Cewar Koeman

Gakpo Ya Yi Gaggawar Koma Wa Liverpool, Cewar Koeman

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Boko Haram Sun Kashe Mutum Dubu 100 Tare Da Tarwatsa Mutane Miliyan 2 —Irabor

Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor

October 12, 2025
Yadda Ake Gurasa Ta Semovita

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita

October 12, 2025
Daga Karshe Tawagar Super Eagles Ta Sauka A Uyo Bayan Saukar Gaggawa A Angola

Daga Karshe Tawagar Super Eagles Ta Sauka A Uyo Bayan Saukar Gaggawa A Angola

October 12, 2025
Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa

Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa

October 12, 2025
Ko Afirka Za Ta Samu Kujerar Dindindin A Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya?

Ko Afirka Za Ta Samu Kujerar Dindindin A Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya?

October 12, 2025
Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 

Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 

October 12, 2025
Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza

Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza

October 11, 2025
Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal

Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal

October 11, 2025
Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata

Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata

October 11, 2025
Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.