A ranar Larabar data gabatane da misalin karfe 2 na ranar dubban magoya bayan maigirma Kwamishinan ya yan jam iyar APC na karamar hukumar Faskari dake jihar katsina suka raka Kwamishina Alhaji Hamza Sule Wamban Faskari a kwatun da yake zabenshi na kofar gidan sarkin Yamma dake cikin garin Faskari domin ya sabunta rijistar shi a jam iyar APC A lokacin da yake jawabin nuna godiyarshi ga dubban magoya bayan shi kuma ya yan jami’yar APC saboda gagarumin tarbar da yasamu daga wurin magoya bayan jam iyar APC yace babu shakka wannan ya nuna cewar jam iyar nan itace jam iyar Al ummar karamar hukumar Faskari dama jahar katsina baki kuma kowa yasan jam iyar APC a keyi a Najeriya Wamban na Faskari yaci gaba da cewar babu abinda zai ce ma sai godiya ganin yadda mutane ke fitowa domin su sabunta rijistar su wasu Kuma yanzu ne shekarun ya kai na jefa kuri insu ya godema maigirma Gwamnan jahar katsina Ahaji Aminu Bello masari Wanda yake kokari wajen magance matsalar tsaron da ya addabi wadansu yankin jahar katsina wannan ya dami Gwamnatin jihar katsina Kuma insha Allahu abin zaizo karshe Kuma kowa yasani wannan matsalar ta rashin tsaron gadarta a kayi tun lokacin mulkin PDP a lokacin da tsohon Shugaban kasa Godluck Jonathan ya kawo ziyarar aiki a Nan jahar katsina inda a ka kashe mana jama a da yawan gaske Kuma a ka lalata dukiyoyinsu daga nan yayi addu a Allah yakawo Mana karshen wannan matsalar tsaron da ya addabemu Alhaji Hamza Sule yacigaba da cewar babu shakka maigirma Gwamna yasha zubar da hawayen sa yadda yadda yan ta addar keyin wannan ta addanci ya kuma kara nuna godiyarshi ga maigirma Gwamna yadda ya gudanar da manyan aiyuka a karamar hukumar ta Faskari dama jahar baki daya ya ce ba a taba samun Gwamnatin da ta taimaki talaka kai tsaye kamar Gwamnatin APC Babu shakka ansami gagarumin fitowar jama a a wasu mazabun da tawagar Wamban na Faskari yakai ziyara kamar irinsu mazabun Faskari Yankara Sheme Ruwan godiya Daudawa da Mairuwa da dai sauran wadansu a kwatunan da a ke sabunta katin rijistar jam iyar Shima Shugaban jam iyar APC na karamar hukumar Faskari Alhaji Hamisu Daudawa ya sabunta katin jam iyar nashi a mazabar shi dake Daudawa Shima tsohon Shugaban karamar hukumar Faskari Kuma Mai jiran gado Alhaji Bala Ado Faskari da shugaban matasan jam iyar APC na jihar katsina Alhaji Hamza mamman sheme dukkansu sun sabunta katin jam iyar tasu a mazabun su Kuma sun yaba da fitowar jama a kuma sun nuna godiyarsu ga Gwamnatin jihar katsina Kuma sunyi kira ga uwar jam iya ta kasa da su karo rijistar ganin tayi kadan saboda yawan magoya baya da jam iyar take dasu a kasar musamman a nan jahar katsina Wadanda suka rufama tawagar ta Wamban Faskari baya sune Shugaban jam iyar APC na karamar hukumar Faskari Alhaji Hamisu Daudawa da Shugaban matasan jam iyar Alhaji Hamza mamman sheme da tsohon kantoman karamar hukumar Faskari Alhaji Bala Ado Faskari da tsohon Dan majalisar tarayya dake Abuja Alhaji jafaru Balarabe yarmalamai da tsohon Dan majalisar dokokin jahar katsina Alhaji Isa Abubakar da Danmasanin Yankara Alhaji Aliyu Musa Yankara da want na hannun daman Wamban Faskari Alhaji lawal salimu da tsofaffin kansilolin na karamar hukumar Faskari da sauran manyan yan jam iyar APC na karamar hukumar Faskari
Ibrahim Musa Dankwairo: Sarakuna Sun Kyale Makadan Fada A Lalace
Makadan Fada na yanzu sun shiga wani hali mai ban...