Kwamishinan ‘Yansanda na Babban Birnin Tarayya (FCT), CP Ajao Adewale, ya gargadi jami’an ‘yansanda da na kula da zirga-zirga kan yin tsalle cikin motocin da ke tafe ko kuma jan sitiyarin direbobi, yana mai bayyana irin wannan hali a matsayin abin da bai da tsaro, bai dace ba, kuma yana lalata mutuncin Rundunar ‘Yansanda ta Najeriya (NPF).
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yansandan FCT, SP Josephine Adeh, ta fitar a Abuja, ta ce Kwamishinan ‘Yansanda ya yi Allah-wadai da dabi’ar rashin kwarewa ta jami’an zirga-zirga na yin tsalle cikin motocin masu karya doka ko kuma yunkurin kwace sitiyarin direbobi. CP ya bayyana irin wadannan ayyuka a matsayin masu hadari, da ba za a aminta da su ba, kuma ya sabawa ka’idojin aikin ‘yansanda.
Adeh ta ce CP ya kuma sanar da kaddamar da aikin musamman mai suna Operation Keep Traffic Flowing, inda aka kafa tawagar sa ido domin tabbatar da bin wannan umarni, tare da gargadin cewa duk jami’in da aka samu yana keta wadannan dokoki za a hukunta shi.
“CP ya bayyana fara aikin gaggawa na Operation ‘Keep Traffic Flowing’, kuma ya kafa tawagar sintiri domin bibiyar ayyukan jami’an zirga-zirga gaba kaya, tare da umarni na musamman kan kama duk wani jami’i da aka samu da karya wannan doka,” in ji ta.
Hakazalika, CP ya bayyana muhimman wuraren da ke da cunkoson zirga-zirga a Abuja, ya kuma gargadi jami’an sintiri kan gujewa dabi’ar rashin kwarewar yin tsalle cikin motocin masu laifi.
A jawabin da ya yi wa shugabannin sashen sintiri, jami’an ‘yansandan motoci, da sauran jami’an da ke aiki a hedikwatar rundunar, CP ya ce halayen jami’an sintiri a fili suke bayyana hoton da al’umma ke da shi game da rundunar ‘yansanda.
Adeh ta bayyana cewa CP ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jami’ai ke gudanar da ayyuka a halin yanzu, yana mai jaddada cewa kula da zirga-zirga na daga cikin manyan alamomin nuna ci gaban gari.
Bayan ya yi yawon duba wurare da dama a birnin a lokutan cunkoso, CP ya gano muhimman wurare kusan 30 da ke da matsalar zirga-zirga, ciki har da Wuse, Area 1 Roundabout, Jikwoyi, Karu, Kurudu, AYA, Apo Resettlement, Gudu, Galadima, Dawaki, da Kubwa.
Ya umarci jami’ai da su kasance a bayyane a wadannan wurare domin tabbatar da tafiyar zirga-zirga yadda ya kamata.
“CP Adewale ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda jami’an sintiri ke gudanar da aikinsu yanzu, yana mai jaddada bukatar sabuwar fahimtar aiki. Ya ce harkar sintiri na daga cikin muhimman alamu na auna tsari da ci gaban gari, yayin da jami’an zirga-zirga suke kasancewa hoton farko da jama’a ke gani daga ‘yansanda.
“A kan haka, ya gargade su da su kiyaye ladubban aiki da bin doka, su guji duk wani hali marar kyau da zai iya bata sunan rundunar gaba daya da kuma na FCT musamman,” in ji PPRO.
Ya kuma roki mazauna birnin da su bi dokokin zirga-zirga, su mutunta jami’an da ke bakin aiki, su kuma guji bayar da cin hanci, wanda ya bayyana a matsayin abin da bai dace ba. Ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kasancewa a fili tare da tabbatar da ingantacciyar tafiyar zirga-zirga a FCT.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp