Kwamitin kula da harkokin wajen na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC), ya fitar da sanarwa kan amincewa da kudurin da majalisar dattijan Amurka ta yi na “Kuduri game da batun balan-balan dinta maras matuki” a jiya Litinin cewa, wannan mataki ne na nuna son rai da wuce gona da iri na “barazanar Sin” da munanan hare-hare don neman bata sunan kasar Sin. Kuma wannan aikin kuskure ne da bangaren Amurka ya yi don yunkurin kara matsin lamba ga bangaren Sin, bayan da majalisar dattawa ta Amurka ta zartas da irin wannan kuduri.
Bangaren Sin ya bukaci majalisar dokokin Amurka da ta mutunta gaskiya, da ka’idojin dokokin kasa da kasa, da na yau da kullum da suka shafi huldar kasa da kasa, da daina yin katsalandan a kan kasar Sin, da kuma kaucewa kara ruguza da lalata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. (Safiyah Ma)