Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa fasinjoji 16 daga Arewacin Nijeriya a Jihar Edo.
Lamarin, wanda ya faru a ranar 27 ga watan Maris, 2025, a garin Udune Efandion na Uromi, ya tayar da ƙura game da gillar.
- An Kama Wanda Ake Zargi Da Kashe Mai PoS A Adamawa
- ‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya bayyana harin a matsayin “rashin adalci”
Ya jaddada cewa duk wani ɗan Nijeriya na da ‘yancin yin tafiya a ƙasar nan ba tare da fargabar cin zarafi ko tsangwama ba.
“Abin da kowa ya sani shi ne, ya zama wajibi a bar ‘yan kasa su yi tafiya a duk faɗin kasar nan ba tare da fuskantar wata barazana ko cin zarafi ba,” in ji shi.
Kwankwaso ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da cewa an hukunta masu laifin.
“Ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike a kan wannan lamari mai tayar da hankali tare da tabbatar da an hukunta masu hannu a ciki,” in ji shi.
Tsohon gwamnan ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, da gwamnatin Kano da sauran jihohin da abin ya shafa, tare da yin addu’ar Allah Ya jiƙansu.
Kisan ya haifar da cece-ku-ce kan hatsarin da ke tattare da ɗaukar doka a hannu, tare da buƙatar a ƙara inganta tsaro don hana irin haka faruwa a gaba.
Jagororin siyasa da na al’umma da dama sun goyi bayan kiran da Kwankwaso ya yi na neman adalci, tare da buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa a kan waɗanda suka aikata wannan ta’asa.
Yayin da bincike ke ci gaba, ana ci gaba da matsin lamba kan hukumomin tsaro don tabbatar da cewa an yi adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp