Kasa da sa’o’i 48 da sanar da kama wata kwantena É—auke da makamai da aka shigo da su kasar nan ba bisa ka’ida ba daga Æ™asar Turkiyya, a tashar jirgin ruwa ta Onne a Jihar Ribas, babban Kwanturolan hukumar hana fasa kwauri ta Æ™asa, Bashir Adewale Adeniyi, ya sanar da sake kama wasu tarin makamai a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Makaman wanda kuÉ—insu ya kai Naira miliyan 270, an kama su ne a sashen dakon kaya na tashar jirgin saman, inda bincike ya nuna an shigo dasu ne daga Turkiyya, tare da wani mutum da a yanzu yake a tsare.
- Sin Na Maraba Da Dukkan Matakan Dake Saukaka Dangantakar Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya
- An Gudanar Da Bikin Mu’ammalar Al’adun Sin Da Kazakhstan
A cewar shugaban, jami’ansu da ke filim jirgin sun kuma kama kayan aikin soja da wasu nau’in kayyayakin hukumomi tsaro.
Bisa la’akari da yawan haɗuran da ke tattare da sa ido kan kayan da ake shigowa da su, ya sa hukumar Kwastam ɗin ta wajabatawa kanta nazari sosai kan kwantenonim da ke kawo wa kasar nan.
An gano kwantenar na É—auke da bindigogi guda 844 da harsasai 112,500 da aka shigo da su cikin kasar nan daga Turkiyya.