Hukumar Kwastam a Jihar Kano da Jigawa ta samu kudaden shiga har Naira biliyan 52.7 a shekarar 2023.
Kwanturola Ibrahim Chana ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Legas.
- Majalisa Ta Amince Tinubu Ya Ciwo Bashin Naira Tiriliyan 7.5
- Asalin Yadda Aka Samo Sunan Hausa Bakwai Da Banza Bakwai
Chana ya ce kudaden shigar ya nuna karuwar kashi 26.4 cikin dari idan aka kwatanta da Naira biliyan 41.7 da aka tara a shekarar 2022.
Ya kara da cewa hukumar ta yi kyakkyawan aiki a shekarar da ta gabata ta fuskar samar da kudaden shiga, saukaka harkokin kasuwanci, da yaki da fasa kwauri idan aka kwatanta da 2022.
A cewarsa, hukumar ta samu ci gaba bayan wayar da kan jama’a da kuma hada kai da ‘yan kasuwa a jihohin Kano da Jigawa.
Daga cikin kayayyakin da suka kama suka hada da fatar jaki, tabar wiwi, magunguna marasa rajista wadanda aka mika su ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa.
A game da gudanar da harkokin kasuwanci, ya ce hukumar ta hada kai da sauran hukumomi don inganta aiki a tsakanin masu ruwa da tsaki daban-daban.
Chana ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi a shekarar 2023, ya mayar da hankali ne kan ci gaba da ci gaban yankin Maigatari a jihar.