Kyakkyawar Tarbiyya Ta Sa Gawuna Ba Shi Da Abokin Hamayya A Kano – Ambasada Dandago

Ambasada Mansur Haruna dandago, Shugaban kungiyar Ganduje/Gawuna Ambasadas, jami’in yada labaran kungiyar Kasuwar Kantin Kwari, guda cikin matasan dake yawan fashin baki kan siyasar Jihar Kano. A tattaunawarsa da wakilinmu a Kano Abdullahi Muhammad Sheka, dandago ya bayyana kyakkyawan fatan da ake wa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Nasiru Yusif Gawuna tare da bayyana wasu muhimman abubuwan da ya banbanta da sauran. Ga dai yadda Tattaunawar ta Kasance.

Bari mu fara da jin wanda muke tare da shi?

Alhamdulillah ni sunana Ambasada Mansur Haruna dandago Shugaban kungiyar Ganduje/Gawuna Ambasadas Kuma kakakin kungiyar ‘Yan Kasuwar Kantin Kwari.

Ganin yadda tukunyar siyasar Kano ta fara tafarfasa, an fara jin duriyar masu zawarcin kujerar Gwamnan Jihar Kano, shin ko me za ka ce kan haka?

Gaskiya ne amma kamar yadda ka sani kamar abinda bahaushe ke cewa halin mutum jarinsa, Jihar Kano ce ke zaman fitilar siyasar Nijeriya, wannan tasa ba haka kawai Kanawa ke zabar wanda zasu damka amanarsu a hannunsa ba. Wannan tasa kake ganin a Kano ne aka hakkake cewa daga liman sai na’ibi. Anga yadda Tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau ya ja nasa zamanin da Mataimakin sa, haka shima Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wuf ya damka ragamar Jihar Kano a hannun Khadimul Islam.

Kenan kuna ganin shi ma Gwamna Ganduje nasa mataimakin zai mikawa?

Ina son tabbatar maka da cewa tunda ake Mataimakin Gwamna a Jihar Kano ba a taba Mataimaki mai hakuri, biyayya, dattako da mutunta Jama’a kamar Dakta Nasiru Yusif Gawuna ba. Wannan kuma Jama’ar Jihar Kano shaida ne, musamman yadda Gwamna Ganduje ya aminta da nagartar Gawuna, anji yadda Gwamnan ke jero yabo da Jinjina alokacin karbar wata lambar Karramawa da aka baiwa Ganduje.

Wadanne abubuwan za ka bayyanawa Jama’a da kake ganin sune sirrin kyakkawar dangantakar dake tsakanin Gwamna Ganduje da mataimakinsa?

(Dariya) ‘yan jaridar kenan, kyakkawar tarbiyya da Gawuna ya samu daga iyaye itace fitilar da ke haska rayuwarsa. Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya fito daga gidan girma, jikan Shehu Hassan na Gawuna ne, wannan tasa yake da nagartacciyar tarbiyya, mutunta Jama’a ga yakana da sanin ya kamata. Wannan ce tasa Gawuna ba shida abokin hamayya domin ya samu shaidar mutunta Jama’a da kaunar hadin kai da zaman Lafiya.
Haka zalika, Dakta Nasiru Yusif Gawuna yake kyakkyawar fahimta da daukacin kunguyoyin addini ko darikun da ake dasu a Jihar Kano, zaka yarda dani musamman ganin Gawuna yana da ingantacciyar alakar mutunta juna da darikarTijjaniyya, wanda Kakansa Shehu guda, sannan haka lamarin yake a gidan kadiriyya, Izala ma haka suke mutunta shi yake mutuntasu. Saboda haka Gawuna kadai zaka tsayar takara a JIhar Kano, kaci zabe cikin salama da aminci.

Ambasada Karka manta an fara jin duriyar masu zawarcin wannan kujerar akakar zaben Shekara taz 2023?

Gaskiya ne, amma Kanawa suna da wani ma’auni da suke Jinjina duk wani mai bukatar jagorantarsu, sannan kuma a iya sani na zaman lafiyar Jihar Kano ne babban abin fata garemu, idan kuwa haka ne, lallai Gawuna shi ne amsa. Dalili na shi ne tarihi ne ke maimaita kansa. Nagartar Dakta Nasiru Yusif Gawuna ce ta bashi bashi damar Shugabantar karamar Hukumar  Nasarawa har Karo biyu.

Bayan haka kuma Malam Ibrahim Shekarau haka ya yi Gwamnatin sa dashi, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso shima har kwamishinan Ma’aikatar gona ya yiwa Gawuna. Da Allah ya baiwa Ganduje ragamar jagorancin Jihar Kano, shima a zangon farko sai da ya bashi mukamin Kwamishina, daganan kuma ya nada shi a matsayin mataimakinsa. Duk wannan wata ‘yar manuniyace daga Allah. Ba kowa Allah ke hadawa irin wannan baiwar ba sai wanda ya yi dace kuma wandaya rabu iyaye lafiya.

Haruna dandago gwari gwari mene banbancin Gwanin naka da sauran masu sha’awar wannan mukami?

Na farko gaskiya, amana, hakuri, biyayya, kaunar hadin kai da fahimtar juna,  sannan kuma Gawuna ne dan takara daya tilo da ba shida abokin hamayya, kuma ina tabbatar maka da cewa, Dakta Nasiru Yusif Gawuna shi ne Gada kuma shi ne allurar dinke duk wata baraka. Musamman ganin ya yi aiki da Shekarau, ya yi aiki da Kwankwaso sannan kuma yanzu haka yana aiki da dattijon arziki kuma Khadimul Islam Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Wadannan da ma sauran abubuwan da lokaci ba zai barni nayi gudu hard a zamiya wajen warware zare da abawar karamar da Allah ya yiwa wannan bawa ba, amma dai a sani Gawuna alhairi ne.

Tsayar da Gawuna wannan takara tamkar lashe zaben ne kai tsaye, domin bashi da makiya a fili da ko a boye. Irin kyakkawar aniyarsa ce tasa duk wani aiki da ake fatan samun nasarar sa, sai kaga Gwamna Ganduje ya damka jagorancinsa a hannun Gawuna. Dubi batun Kwamitin yaki da annobar Korona, saboda jajircewarsa har sai da aka damka lambar Karramawa ga Gwamna Ganduje a matsayin Gwamnan da ya zarta saura damarar fatattakar annobar daga doron kasa. Haka kwanan nan aka kammala Musabakar Al’kur’ani Karo 35, Kuma Shi Gwamna ya nada Shugaban Kwamitin shirye shiryen taron Musabakar da Jihar Kano ta karbi bakuncin ta. Kuma aka samu gagarumar nasara.

Misali ace Gwanin naka yaki amincewa da yin takara, shin Ina mafita?

Kotu zamu dunguma, domin ai Kanawa suna da hakkin kiran duk wanda suka yarda da amanarsa, don haka idan ya nuna kin amincewa da bukatar al’ummar Jihar Kano, to lallai bamu da zabi illa durkusawa gaban kotu. Wanda kuma muna da yakinin ma bazai kaucewa bukatar Kanawa ba.
Wani abin sha’awa ga Dakta Nasiru Yusif Gawuna shi ne bai taba sha’awar shiga cikin kowane rikici da ka iya kawo rabuwar kawunan al’umma ba, sannan kuma shi ne mutun daya dake rike kujera lamba biyu a Jihar Kano, amma kullum yana hanyar ta’aziyya, daurin aure, dubiyar marasa lafiya. Kyakkyawar danganta da son alkur’ani yasa Majalisar Mahaddata Alkur’ani ta kasa zabarsa tare danada shi a matsayin Garkuwan  Mahaddata Alkur’ani na kasa. Wannan ba karamar karramawa bace, domin alarammomi ba ‘yan siyasa ba ne, sai wanda suka tabbatar da nagaratarsa suke mu’amalar amana dashi.

Kai ne shugaban kungiyar  Gaduje/Gawuna Ambasadas, shin me kuka sa gaba zuwa yanzu?

Alhamdulillahi kamar yadda kowa ya sani wannan kungiya ce data kudiri aniyar yayata kyawawan manufofin Gwamnatin Dakta Abdullahi mar Ganduje, kuma muna kara yiwa Allah godiya ko hasidin ia hasada  bai isa kalubalantar Gwamnatin Ganduje da rashin ayyukan raya kasa ba, sannan kuma kasha 80% na ayyukan da Ganduje ke shimfidawa Kanawa ido na iya ganinsu, hannu na iya tabawa ya yinda kafa  zata iya takawa. Batun kawata Birnin Kano kadai ya isa a jinjinawa  Ganduje, balle kuma a tabo batun ilimi Kyauta, karin masarautu, samar da cibiyar horar da sana’u, gina manyan gadoji irin wadanda manyan kashen duniya ke yayinsu.

Haka kuma samun mataimakin da Ganduje ya yi masanin makamar aiki, mai hakuri da sanin ya kamataa, mai  kyakkyawar alaka da dukkan bangarorin al’ummar Jihar Kano, ya karawa Gwamnatin tagomashi, wannan bakaramar baiwa bace daga Allah, don haka wannan kungiya ta himmatu wajen fadakar da duniya irin romon demokaradiyyar da Kanawa ke sharba.

Wane sako ne dakai ga al’ummar Kano, musamman kan batun makomar Jihar Kano a Shekara ta 2023?

Sako na bai wuce kiran al’ummar Kano ba, tare da nushe su alfanun wannan bawan Allah, kamar yadda kowa ya sani Gawuna baya gudun Jama’a kamar yadda suma Jama’ar basa gudunsa. Lallai akwai bukatar Jama’a su kara bude idanuwansu domin yiwa duk wanda ke neman sahalewarsu kallon tsanaki, su san wane shi, daga wane gida ya fito mece tarbiyyarsa.

Mun gode kwarai
Nima na gode

Exit mobile version