Annabi (SAW) don ya tabbatar wa al’ummarsa cewa, dabi’un Annabawa da su ake haifarsu ba koya suke ba, dabi’ar Dan’adam duk irin al’ummar da ya taso, irin halayyar wurin zai taso da ita, sai da gabaya in ya shiga Duniya ya sauya, shi ya sa Allah ya ce, kowa a kan tafarkin Addini yake, sai daga baya iyayensa su sauya masa da wanda suke kai.
Amma Ubangiji ba zai tuhumi kowa ba a kan abin da iyayensa suka sauya masa sai in ya balaga an masa wa’azi bai sauya zuwa tafarkin addini ba.
- Kyawawan Halaye 2: Wasu Annabawa Da Sauran Bayin Allah Da Suka Yi Magana A Tsumman Jego
- Matan Annabi Muhammadu (SAW)
Annabi (SAW) yana cewa, yayin da na taso sai Allah Ubangiji ya sanya min kiyayyar gumaka da kin wake (sai in ta Addini, sabida yana (SAW)a a yi ta Addini kuma a wasu hadisai ya ambaci wasu wakoki da aka yi na addini kuma ya yi ta’aliki a kansu). Haji Mushri, almajirin Shehu Ibrahim Inyas ya ce ya kirga baitin Annabi (SAW) na Shehu Ibrahim a bakin Aliyu Sha’ir 10,000 da ya yi wa Annabi (SAW). Wanda ya yi Littafin wakokin Shehu Ibrahim (Afakush Shi’iri) ya ce yana da baitin Shehu Ibrahim Da ya yi wa Annabi (SAW) 11,000.
Annabi (SAW) ya ci gaba da cewa, duk wani aiki da jahiliyya ke aikatawa kafin zuwan Musulunci an samun kiyayyarsa, ban taba nufin in aikata ko daya ba sai sau biyu, shi ne kidan biki (duk lokacin da na yi nufin zuwa sai bacci ya dauke ni, sai dai in farka in ji labarin an gama har sau biyun) wanda kuma Shari’arsa ta halatta da fadinsa cewa. Ku banbanta bikin alkairi na farin ciki da wanda ake boye-boye. Bikin alkairi da aka yi kida a cikinsa ko kuma taro irin na al’ada, duk wanda ya zo shigewa zai tambaya, me ake yi ne, sai a ce ai wacce ce take biki amma in ba na alkairi ba ne sai ka ga ana boye-boye a cikin bikin.
Sabida haka, kyawawan dabi’u da hasken sanin Allah, halittar Annabawa ce ba koyanta suke yi ba amma bayin Allah dole sai sun hadu da masana Ubangiji sai su kama hannunsu su zama tsani zuwa gare shi. Duk da cewa har Annabawan suna kara tarakki zuwa ga Ubangiji sabida Allah ba shi da iyaka; Annabi Zakariya’u sai da ya hadu da Sayyada Maryam uwar Annabi Isah (A.S) ya kara tarakki – huna lika da’a zakariya’u Rabbah, Annabi Musa sai da ya hadu da Kadiru – kala hal attabi’uka ala an tu’allimani mimma ullimta rushdah…
Allah ya fada cikin hakkin Annabi Yusuf “walamma balaga ashuddahu a tainahu hukman wa ilma…” yayin da Annabi Yusufa ya kai shekrun Balaga, mun bashi sanin Allah da Ilimi.
Akwai wadanda kuma ba Annabawa ba amma Allah ya ba su wasu daga cikin kyawawan dabi’un Annabawa tun suna ‘yan yara ko kuma da su aka haife su. Don haka Allah ya zama Ubangiji ba a yi masa ka’ida, yana ba ma wanda yake so a lokacin da ya gadama a kan wanda ya gadama ba tare da wani dalili ba. Sanya wa Ubangiji ka’idodi kamar takure shi a wuri daya ne da fadin wasu malamai cewa, Allah ba zai yiwu ya yi kaza da kaza ba, kamar Allah ba shi da iko mudlaki kenan.
Shehu Ibrahim Inyas yana cewa, ba don nufin malaman da suke cewa, Allah ba ya nan kuma ba ya can sai dai wani wuri kayyadajje, girmama shi ba ne da duk ‘yan wuta ne.
A cikin wadanda ake haifa da kyawawan dabi’a daga cikin bayin Allah, akwai yaron da ke zuwa da sadaukantaka, wani gaskiyar zance, wani kyauta, wasu kuma kishiyoyin halayen da muka ambata – Ragontaka, Karya, Rowa. Daga bisani kuma, malamai ko duniya ta sa mutum ya koya wasu dabi’u kyawawa ko kuma ya sauya a kan wadanda aka halicce shi da su.
Don haka a wurin bayin Allah, babu wani wanda za a ce ya fi karfin ya shiryu. Akwai misalin wata kissa ta wata Mata da ta zo wurin Annabi Musa ta tambaye shi, Allah ya rubuta ni cikin masu haihuwa? Annabi Musa bayan ya gana da Ubangiji ya tambaye shi, ya Ubangiji baiwarka wacce tana tambaya ko tana cikin wadanda aka rubuta za su haihu, Ubangiji ya ce masa ba ta ciki, Annabi Musa ya dawo ya isar mata da sako cewa ba a rubuta ta cikin masu haihuwa ba. Wani bawan Allah yana zaune ya ji abin da ke faruwa, sai ya kira ta ya ce mata baiwar Allah kin yi kuskure, ina ruwanki da sanin abin da Allah ya rubuta miki, kawai ki yi addu’a ki ce Allah ya ba ki, zai ba ki. Haka kuwa aka yi, sai ga mace ta haihu da yara biyu da wani sabon juna-biyu a tare da ita, wannan baiwar Allah sai suka hadu da Annabi Musa ta bashi labarin cewa duk wadannan yaranta ne ga na Uku a ciki, Annabi Musa sai ya koma wurin Ubangiji ya ce ya Rabbi ga abin da ka fada min na gaya wa matar kuma yanzu ga ‘ya’ya ta samu, sai Ubangiji ya ce kai tambaya ta ka yi, bawana wane kuma roko na ya yi sai na share hukuncina “yamhullahu ma yasha’u wa yusbit…”
Sabida haka, don Allah ya halicci mutum da munanan dabi’u, in aka hada shi da zikirai Allah mai iko ne ya sauya masa da kyawawan dabi’u. “Wa kullun muyassarun lima kulika lahu” kowa ana sauwake masa abin da aka halicce shi don shi. “fa’amma mana a’ada wattaka, wa saddaka bilhusna, fasanuyassiruhu lil Yusra, wa amma man bakhila wastagna, wa kazzaba bil husna, fasanuyassiruhu lil usra” Amma duk wanda ya bayar da kyauta, ya ji tsoron Allah kuma ya gasgata kyautaye (Ma’arifa ko kiyama) sai mu sauwake masa bin lamarin Allah, zai ga abin da sauki. Amma wanda ya yi rowa ya nemi wadata da hakan kuma ya karyata kyautaye (Ma’arifa ko kiyama) sai mu sauwake masa wahala – kullum ya ce aikin ba zai yiwu ba duk alkairi sai ya karyata.
Sabida haka, magabata suka samu sabani a cikin wannan magana ta sabanin halaye da cewa: shin wadannan halaye halitta ce da ba za a iya kore su ba, in mutum na Allah ne haka yake, in Mutum na banza ne haka yake ba zai iya sauyawa ba ko kuma Mutum na iya zama na Allah sabida kokarinsa kuma yana iya zama na banza sabida sakacinsa?
Imam Dabri ya ruwaito daga magabata cewa dabi’u masu kyau halitta ce daga Allah, dabi’u ne da Allah ya halicce su a jikin bawa. Mai littafi (da muke karantawa), Imam Alkadi Iyad yake cewa, dabi’u kyawawa a wurin Annabawa, halitta ce daga Ubangiji amma a bangaren bayin Allah, an halicce su da wasu, wasu kuma sai sun yi tsururunsu da Azkarai, sabida Allah ya halicce mu ne da shirin zama na Allah da na banza da fadinsa “Lakad kalaknal insana fi ahsani takwim, summa radadnahu asfala safilin” lallai mun halicci dan Adam a kan mafi tsarin tsayuwa sannan muka maida shi kaskantaccen kaskantattu. Sabida an sa masa shirin zai iya ci gaba da irin yadda aka halicce shi kuma zai iya sauyawa ya zama na banza “wa hadainahun najdain” mun shiryar da shi hanyoyi biyu.
Allah ba ya zaluntar bayinsa, ya haliccesu a kan ba daidai ba kuma ya azabtar da su, Allah ba ya haka, ya shiryar da Dan Adam hanyoyi biyu ya zaba.
Sai dai kuma, Allah Ubangiji mai yin yadda yake so ne, duk munin dabi’a, ban da karya da ha’inci Allah zai iya halittar Mu’umini a kanta. A wani hadisi an tambayi Annabi (SAW) cewa ko Mu’umini zai iya aikata wasu laifuka kamar yin Zina da Sata da maye yace ‘Eh’ amma ba zai iya yin karya ba da ha’inci. Sabida munin karya da ha’inci. Gaskiya za ta jawo masa barin duka wasu munanan dabi’u.
A wani Hadisin Sayyadina Umar an ruwaito yana cewa “Sadaukantaka da ragontar zuciya, dabi’u ne na halitta da Allah yake sanyawa a cikin zukatan mutane ta irin yadda ya so.”
Wadannan dabi’u abin yabo kuma masu kyawu, suna da yawa amma za mu maida hankali kan asalinta ko kuma mu ce tushenta, don tabbatar wa halittu cewa dukkkansu, Annabi (SAW) ya dabi’antu da su kuma ya hakikantu da su.