Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Alexandre Lacazette, ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Lyon, ba tare da an biya kudi ba, shekaru biyar bayan yabar kungiyar zuwa Arsenal.
Dan wasan mai shekara 31 a duniya ya koma Arsenal ne a shekara ta 2017 akan kudi fam miliyan 47 kuma a wannan kakar ta shekara ta 2021 zuwa 2022 kwallaye hudu kacal ya zura cikin wasanni 30 wanda hakan yasa kungiyar take ganin akwai bukatar ta rabu dashi.
Lacazette dai ya buga wasanni 206 a Arsenal inda ya zura kwallaye 71 sannan ya taimaka aka zura guda 36 sannan ya buga wasanni 16 a tawagar ‘yan wasan kasar Faransa.
Tuni dai Arsenal ta fara zawarcin wanda zai maye gurbin Lancazette inda ta fara tattaunawa da Manchester City domin daukar Gabriel Jesus wanda shima yake fatan barin Manchester City din, bayan kungiyar ta dauki Erling Braut Halland daga Dortmund.