Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KANNYWOOD

Laifin Rahama Sadau, Afakallah Da Kannywood

by Muhammad
November 30, 2020
in KANNYWOOD
9 min read
Kannywood
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Ali Abubakar Sadiq

 

samndaads

Tun asalin Jaruma Rahama Sadau ’yar rawar gala ce kafin Jarumi kuma Darakta Ali Nuhu ya kyalla ido ya hango ta da fahimtar cewa, wannan yarinya za ta iya zama wata gagarumar jaruma. Kasancewar Alin ne ya kawo ta masana’antar hadi da cewa ta iya ‘acting’, kafin ka ce me, ta fara samun shahara yadda ta dusashe wasu taurari mata. Cikin abubuwan da su ka daga likkafar wannan yarinya a ka san ta sosai bai rasa nasaba da kutsa kanta cikin rigingimu iri-iri tun shigowarta wannan masana’anta ta Kannywood, watakila ta na ganin cewa ta hanyar saka kanta cikin rikice-rikice su ne za su dauwamar da tauraronta a sama ba tare da la’akari da irin al’ummar da ta sami kanta a ciki ba.

Rikicin baya-bayan nan ba shi ne na farko ko na biyu ko na uku ko hudu ba; shi ne rikici na biyar da ta sami kanta, idan za mu iya tunawa. A farkon shigowarta masana’antar Kannywood ta samu rikici da babban Jarumi Adam Zango yayin da a ka yi zargin ta je wajen da ya ke daukar wani fim nasa kuma ta tashi aikin tare da yin fashe-fashe, abinda ya kai su ga gurfana gaban kwamitin ladabtarwa na MOPPAN (wato Babbar kungiyar masu shirya finafinan Hausa), inda a karshe ta bada hakuri da alkawarin ba za a sake ba. Rahama ta sake samun kanta cikin wani rikicin, inda wani mai shirya finafinai a Maiduguri ya dauke ta a matsayin jaruma, amma sakamakon sabani da su ka samu ta je ta dauko ma sa sojoji, wadanda su ka zo wajen daukar fim din su ka hargitsa shi yadda aikin bai yiwu ba. An ce sakamakon bakin cikin wannan asara da Rahama ta jaza ma sa ya sa ya yi hadarin mota a hanyarsa ta dawowa, inda ya mutu.

Ba dadewa da korarta ba sai ta sami gayyatar shahararren mawakin Amurka, Akon, tare da hadin gwiwar mai shirya fim na Nollywood, Jeta Amata, zuwa cibiyar fina-finai ta duniya, wato Hollywood. Akon ya sanar a shafinsa na Tiwita cewa, “ya kamata mu karfafi matanmu da azama su zuwa cigaba, karbar su, ya fi korar su” a matsayin wani shagube ga kungiyar MOPPAN. MOPPAN ta mika wannan hukunci na korar Rahama ga Babban Daraktan Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, wato Isma’il Afakallah, wanda ya saka hannun amincewa.

Bayan nan sai Rahama ta cigaba da harkokinta a wajen Kano, ganin yadda likkafarta ta daukaka kuma ta cigaba da yin harkokin fim nata na kanta da kuma a masana’antar Nollywood. Bayan lokaci ya ja sai Rahama ta fara kokarin yadda za ta dawo Kannywood a yafe ma ta, kamar yadda wani jami’in MOPPAN ya shaida min a Kano cewa, ta yi kokarin bai wa wani jami’in MOPPAN cin hanci na Naira 50,000 (kodayake ba a tabbatar ba), domin ya hada ganawarta da masu ruwa da tsaki a MOPPAN ko Allah zai sa su yafe ma ta, ta dawo cikin masana’antar, abinda ya ki ya yi.

Kimanin shekara guda bayan hakan, sai hukumar tace finafinai a karkashin jagorancin Afakallah ta sanar da yafe wa Rahama, duk da cewa, kungiyar MOPPAN ba ta amince da matakin hakan ba. Wannan daurin gindi da ta samu daga wajen hukuma ya ba ta damar dawowa gadan-gadan harkokin fim; lamarin da ya haifar da gagarumin sabani tsakanin kungiyar a Jihar Kano da hukumar.

Katsam a makon da ya gabata sai ga shi jarumar ta sake jawo wata babbar rigimar, wacce ba ta taba yin irinta ba sakamakon saka wasu hotuna nata da ke nuna tsiraicin bayanta, abinda ya ja wani wanda ba Musulmi ba ya yi kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW). An ce, Rahama ba ta cire ko maida wa mutumin martani ba har na tsawon sa’o’i sama da ashirin. Kuma wasu cikin kawayenta sun yi kokarin hana ta saka wannan hotuna tun asali, saboda sanin yadda za su iya kawo cece-kuce.

A nan ya kamata mutane su sani cewa, a duk duniya, hatta a Amurka da kasashen Yamma, akwai abinda a ke ganin bai kamata a yi shi a idon jama’a ba, wanda ya sa dokar kasashe ke da hukunci kan abubuwa na bai dace ba. Irin wannan doka ta na daukar “Duk wani abu da ya jibanci yada wani abu cikin jama’a da ya danganci batsa, zagi ko abu maras kyawun gani da zai iya tada hankalin jama’a”. Wannan ya sa Kotun Kolin Amurka (kotun da ma ta halasta auren jinsi) ta tabbatar da wannan doka wajen hana furta kalaman zagi/ashar a duk wani shirin talabijin, musamman domin a kare yara masu tasowa.

A shekarar 1984 lokacin da Madonna ta saki bidiyon wakarta ‘Like A Birgin’ ta fuskanci caccakar jama’a har daga fadar Fafaroma. Haka ma wakar ‘Salt N Pepa’ a shekarar 1991, wacce ke maganar jima’i (Lets talk about sed) da kuma wakar TLC ‘Aint too proud to be’ da ire-iren wadannan wakokin duk sun fuskanci suka.

Laifin Rahama a nan shi ne, a matsayinta na Musulma ta san cewa, akwai ka’idar shiga, wacce addini ya tanada a Kur’ani cewa, dole mata su rufe wuraren da za su iya jan hankalin maza, musammam daga kafada zuwa kasan kwauri a duk sanda su ke a bainar jama’a. Hikimar Kur’ani ita ce, rufe wadannan wurare zai rage abubuwa irinsu fyade da sauransu, kuma bude su na iya kawo hadurra da matsaloli, musamman idan mu ka yi la’akari da cewa, ganin bayanta a bude ya sa wani wanda ba Musulmi ba ya yi kalaman batanci ga Annabi Muhammadu. Da ba ta saka wannan hoto ba, ka ga irin wannan batanci da bai faru ba. A matsayin halin da Najeriya ke ciki na matsi da fushin matasa, yadda kwanan nan mun ga yadda zanga-zangar EndSARS ta haifar da mummunar tarzoma, wannan kalamai na batanci na iya rura wutar rikicin addini, wacce ba za ta haifar wa kowa da mai ido ba. Amma dai Babban Sufeton ’Yan Sanda ya yi wuf ya umarci Kwamishinan ’Yan sanda na Kaduna ya gaggauta bincike kan lamarin.

Lokacin da a ka sanar da bai wa Afakallah wannan mukami nasa, na yi matukar farin ciki ganin cewa ya fito daga wannan masana’anta. Don haka na dauka cewa, zai kawo canji da a ka dade a na tsammani a wannan masana’anta, amma daga dukkan alamu ya kasa.

Sanin kowa ne cewa, tsohon Gwamna Kwankwaso abokin masana’antar Kannywood ne kuma ya karfafa ta ta hanyoyi da dama, domin hatta ita wannan hukuma da Afakallah ke jagoranta shi ya kafa ta. Amma a bayyane ya ke cewa, babu wani gwamna da ya jawo ’yan masana’antar cikin gwamnati irin Gwamna Ganduje mai ci (duk da cewa a daya hannun kuma a na yi wa gwamnatinsa kallon ta na yi wa wasu ’yan masana’antar bita da kulli, idan mu ka duba yadda a ka kama Naziru Sarkin Waka da Sunusi Oscar), domin akalla ’yan masana’antar da dama sun samu mukamai a cikin gwamnatin. Bayan Afakallah, akwai Al-Kenana, Yahanasu Sani, Rashida Adamu, Nura Hussein, Ado Baffa (Marigayi), Ali Lilo da Ibrahim Ibrahim.

Masana’antar Kannywood ba ta taba samun irin wannan tagomashi ba, kuma ya ci a ce wadannan jami’ai sun kawo wani gagarumin canji ta hanyar samar da hadin kai da tallafi na gwamnati wajen cigaban masana’antar. Amma abin takaici kusan duk wadannan jami’ai bukatar gabansu su ke yi, domin babu wata hujja a kasa, wacce ta nuna sun kawo wani gagarumin canji.

Shi kansa Afakallah, wanda ke da mafi girman mukami a cikinsu, a bayyane ya ke ya gaza, musamman idan a ka yi la’akari da ikirarin da daya daga cikin jagororin masana’antar, Hamisu Iyantama, ya shaida min cewa, ya kasance shugaban kwamitin farfado da kasuwanci a masana’antar, wanda Afakalla ya kafa. Cikin hirata da shi, ya tabbatar da cewa wannan kwamiti nasu ya lalubo hanyoyi ingantattu wajen farfado da kasuwancin masana’antar, wanda ya durkushe, ta kokarin farfado da sinimomi, musamman gidan sinimar Marhaba, wanda abin bai dore ba. Kuma sun jawo hankulan masu gidajen kallo wajen ganin sun saka nuna fina-finan Hausa a cikin jadawalinsu.

Sannan ya kara da cewa, sun yi kokarin yakar satar fasaha ta hanyar zuwa jihohi da dama, domin jawon hankulan masu rarraba fina-finai su daina karbar kowanne fim sai da takardar shaidar hukumar tace fina-finai. Har ila yau kwamitin ya hada taro da ’yan ‘downloading’ a gaban jami’an tsaro, domin nuna mu su illar satar fasaha. Haka nan sun yi kokarin samar da dandalin yanar gizo, domin tallata fina-finan masana’antar.

Abin tambaya shi ne mene ne dalilin da wadannan kyawawan shirye-shirye ba su kai gaci ba?  Iyantama ya dora laifin kan Afakallah da cewa, bai iya mu’amala da jama’a ba kuma tsawon watannin da su ka kwashe su na wannan aiki hatta dan alawus na zaman aiki ko na tafiye-tafiye hukumar ba ta iya samar mu su ba, yadda da kudaden aljihunsu su ka rika wannan aiki, baya ga ajiye harkokinsu, domin samar wa masana’antar mafita. A cewarsa, rtaron da su ka yi da ’yan downloading da jami’an tsaro ne kadai hukumar ta dauki nauyi. A karshe ma dutse a hannun riga su ka rabu da Afakallah ba tare da nuna wata godiya ba ko tabbatar da abubuwan da su ka kawo domin cigaban masana’antar.

Ya kamata Afakallah ya farka daga barci ya san cewa, sauran shekaru biyu su ka rage ma sa, kuma idan ya gama su, cikin masana’antar dai zai dawo. Don haka ya rage nasa ya yi amfani da lokacin da ya rage ma sa, domin tabbatar da cewa ya bar bayan da zai yi alfahari da ita.

Ita kuwa masana’antar Kannywood, kamar yadda duk sauran al’amuran Hausawa su ke a yau, ta kasance babu wani abu da za a hadu a yi aiki tare, domin gudu a tsira tare; kowa biyan gajeruwar bukatarsa ita ce a gabansa. Idan mu na da hankali, a yau ba mu da wata masana’anta, wacce za ta iya samar wa dimbin matasanmu aikin yi da kudaden shiga kamar Kannywood, domin kamar yadda na taba fada a wani rubutuna a baya, a yayin da marubucin fim ya dora bironsa a kan takarda, daga nan ya fara samar da ayyukan yi da su ka hada da jarumai, masu shiryawa, bada umarni, daukar hoto, masu tacewa, tsara wajen aiki, masu buga takardu, masu ababen hawa na haya, masu otel-otel, madinka, ’yan talla, masu kasuwanci, masu rarraba fim da tallansa, gidajen rediyoyi da talabijin, kai hatta matan aure a gidajensu wadanda ke dafa abinci a kai wurin daukar fim ko bada hayar sutura. Akalla akwai kimanin sana’o’i 26 da ke da alaka da yin harkar fim.

MOPPAN ta gaza wajen samar da ingantaccen shugabanci a kungiyoyin kwararru (guilds) da ke karkashinta, wanda ta hanyarsu za a iya samarwa da ’yan masana’antar tallafi, a karfafa su kuma idan ta kama a ladabtar da su. Yawancin wadannan kungiyoyi karkashin MOPPAN za ka samu a rarrabe su ke yadda da yawa na da shugabanci guda biyu masu hamayya da juna. Ita kanta MOPPAN din mu na iya cewa ba tsaye ta ke da kafufuwanta ba, domin ba ta da ingantattun hanyoyin samun kudin shiga yadda wasu lokatan ko kudin haya ba sa iya biya daga asusunsu.

Ginshikin kowacce masana’antar fim a duniya bayan saka jari ita ce samun ingantacciyar hanyar kyautar karramawa (awards), domin ita ke jawo hankalin masu saka jari, samar da ingantattun fina-finai da kuma tabbatar da gogayya da azama ga duk wanda ke cikin masana’antar wajen ganin ya inganta abinda ya ke yi.

An wayi gari a Kannywood yau babu wata kyautar karramawa ta a zo gani sakamakon guda dayar da a ke zaton za ta kai gaci an bar ta, ta mutu (KannyAward), wadda kenan kuma a yanzu masu jagorantarta baki ne wadanda ba masana’antar ce a gabansu ba, sai dai abinda za su samu daga masana’antar ta hanyar bayar da karramawar. Ita kanta gwamnati Kano da ta na da masu ba ta shawara, da ta ware akalla Naira miliyan 50 duk shekara, domin samar da irin wannan karramawa ta gwamnati, ba don komai ba sai don za ta habaka harkar a masana’antar yadda za ta iya kawo wa jihar masu saka jari, sannan za ta iya samun kudaden shiga ninkin abinda su ka saka duk shekara, idan abin ya karbu; abinda su Afakallah da ’yan uwansa na Kannywood da ke cikin gwamnatin ya kamata a ce tuni sun saida wa gwamnati.

SendShareTweetShare
Previous Post

Masarautar Zazzau: Raddi Ga Malamin Jami’a!

Next Post

Za A Rika Ba Wa Masu Kanjamau Maganin Da Zai Kai Su Wata Uku

RelatedPosts

Izzar So

Umar Hashim Na Izzar So: Gwarzon Jarumina A  2020

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

Na dauki shekaru masu yawan gaske ina kallon  Fina-finan Hausa...

An Yi ‘WUF’ A Kannywood!

An Yi ‘WUF’ A Kannywood!

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Sabon fim ne, wanda ya zo da salon labari mai...

Jarumai

Jarumai 10 Da Tararuwar Su Ta Haska A 2020

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

Kusan a kowacce rana ta Allah daga safiya zuwa yamma,...

Next Post
Kanjamau

Za A Rika Ba Wa Masu Kanjamau Maganin Da Zai Kai Su Wata Uku

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version