Ma’aikatar kare hakkin jama’a ta Sifaniya ta bukaci ofishin mai shigar da kara na kasar da ya binciki dan wasan gefe na Barcelona Lamine Yamal bayan da aka ce ya dauki hayar gajerun mutane zuwa wajen bikin cikarsa shekaru 18 da haihuwa, Lamine Yamal ya shirya liyafa a ranar Lahadi a wani wajen da ya dauka haya a Olibella, wani karamin gari mai tazarar kilomita 50 arewa maso yammacin Barcelona, a cikin wadanda suka halarci bikin akwai masu amfani da shafukan YouTube, mawaka da abokan wasansa a Barcelona da dama.
Ana zargin Lamine Yamal ya dauki hayar gungun masu wasan nishadi da ake kira da (Dwarf) wato wadanni domin nishadantar da mahalarta taron, wani abu da kungiyar mutanen da ke fama da ciwon Achondroplasia da sauran matsaloli na kashi (Skeletal Dysplasias) a kasar Sifaniya (ADEE) suka kira da abin da ba a yarda da shi ba a karni na 21, Darakta Janar na Nakasassu, wani bangare na Ma’aikatar Kare Hakkin Jama’a, ya ce kungiyar ADEE ta shigar da karar akan Yamal.
- Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (6)
- Mutuwar Malamin Jami’a A Otel: Jami’ar Kogi Za Ta Gudanar Da Bincike
Saboda haka, Darakta Janar din ya bukaci ofishin mai gabatar da kara da ya yi bincike domin sanin ko an tauye hakkokin nakasassu ko kuma an keta hakkin nakasassu, ADEE ta ce “Ta fito fili ta yi Allah wadai da daukar wadannin da ke da ra’ayin mazan jiya a matsayin wani bangare na nishadantarwa, kuma ta ce za ta dauki matakin shari’a saboda wannan ka iya zama wata hanya ta nuna wariya a tsakanin nakasassu da sauran mutane a kasar ta Sifaniya da ake yawan samun kararraki na nuna wariyar launin fata,” in ji shi.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce “Wadannan ayyuka ba wai kawai sun saba wa dokokin da ake da su a yanzu ba, har ma da muhimman ka’idojin da’a na al’ummar da ke neman daidaito da mutuntawa, akwai doka game da hakkin nakasassu da ta haramta ayyukan nakasassu a fili kamar aikata ayyukan nishadi a wajen taron jama’a ko wajen bukukuwa, wadanda ake amfani da nakasassu ko wasu masu rashin lafiya wajen yin izgili ko ba’a, wanda hakan ya matukar saba wa dokar mutunta dan’Adam,” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp