Abba Ibrahim Wada" />

Laporta Ya Zargi PSG Da Jefa Barcelona Rudani

Dan takarar shugabancin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona wanda shine ake ganin zai lashe zaben, Joan Laporta, ya zargi kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German da haddasawa kungiyar rudani, sakamakon soma tuntubar kaftin dinsu Lionel Messi.

A makon jiya daraktan wasannin kungiyar PSG, Leonardo ya ce kulla yarjejeniya da manyan ‘yan wasa irinsu Messi shi ne burinsu, yayin da kuma a farkon makon nan, dan wasan tsakiya na kungiyar ta PSG Leandro Paredes ya ce tuni suka soma tuntubar kaftin din na Barcelona don haka a yanzu wuka da nama na hannunsa.
A karshen kakar wasa ta bana yarjejeniyar Messi da Barcelona za ta kare, bayan kokarin katse ta da dan wasan yayi a shekarar bara, abinda ya janyo kai ruwa rana tsakaninsa da kungiyar wanda har yayi sanadiyar tafiya da kujerar shugaban kungiyar Jose Maria Bartemeu.
Tun a kakar wasa ta bara ne kuma ake alakanta Messi da komawa kungiyar PSG ko kuma Manchester City, kungiyar da a waccan lokacin har ta tattauna da maihafin tauraron na dan wasan.
Itama kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta tattauna da mahaifin dan wasan wanda daga baya ya bayyana cewa dan nasa zai cigaba da zaman kungiyar har zuwa karshen kakar wasa ta bana wadda za ta kare a watan Mayun bana.

Exit mobile version