Connect with us

KASASHEN WAJE

Larabawa Sun Musanta Zargin Yi Wa Zaben Amurka Na 2016 Shishigi

Published

on

Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa ta ce ba ta yi yunkurin yin katsalandan a zaben Shugaban Kasar Amurka na 2016 don amfanar Donald Trump ba.

Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa Anwar Gargash ya karyata hakan ta kafar ‘twitter’ jiya Talata bayan da kafafen yada labarai a Amurka su ka ruwaito cewa dan Trump ya gana da Jakadun Saudiyya da Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa a 2016.

“Ya kamata a fuskanci gaskiya a maimakon gugar zana da kuma yada jita-jita. Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta yi yinkurin yin katsalandan a zaben Shugaban kasar Amurka na 2016 ba,” a cewar Gargash. Ya kara da cewa, “Kamar sauran gwamnatocin da ke dasawa da Amurka, jami’an Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa sun tattauna da jami’an yakin neman zaben bangarorin biyu a 2016, don su san inda kowane dan takara ya dosa game da manufofin kasashen waje.”

Jaridar New York Times ta ruwaito a makon jiya cewa dan Trump ya yi wata ganawar da ta kunshi wakilan Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa da Saudiyya. An ce wai wani dan aike ya gaya ma dan Trump cewa a shirye Shugabannin kasashen biyu na Larabawa su ke su taimaka ma mahaifinsa ya ci zabe.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: