Layya da tumaki da awaki ta fi falala a Malikiyya, sannan shanu sai kuma raÆ™uma, amma tumaki sun fi awaki falala. Kuma maza na kowanne jinsin dabbobi da aka ambata ya fi mata falala. Duba; Alma’Å«natu Alã Mazhabi Ãlimil Madinati [1/485] da Arrisãlatu [shafi na 108] da Alkãfi [shafi na 238].
Ana yin layya ne da dabbar da take lafiyayyiya ƙosasshiya, ban da gurguwa da gurguntakarta ta bayyana a fili da mai ido ɗaya da rashin ganin idon ya bayyana a fili, ban da mara mai da ɓargo, ban da mara lafiya da rashin lafiyarta ta bayyana a fili. Duba; Muwaɗɗã Malik tare da Almuntaƙã Sharhul Muwaɗɗã [4/152-153] da Assamarud Dãnī [shafi na 392-393] da Aljawãhiruz Zakiyyati [shafi 144) da Alkãfi (shafi na 238) da Hashiyatud Dasūƙī ( 2/119] da Attaju Wal Iklil [4/336].
WaÉ—annan sifofi guda huÉ—u ijma’i ne a Mazhabar Malikiyya cewa ba a yin layya da duk dabbar da ta sifanta da wata sifa daga cikin sifofin. Duba; Assamarud DãnÄ« [ shafi na 393].
Babba don tana ɗingishi da ba za a iya kiranta gurguwa kaitsaye ba, haka mai gani gararagarara za a iya yin layya da ita. Duba Almuntaƙã
[4/152-153].
Fa’ida: Duk dabbar da take mahaukaciya ko mai É—oyin baki ko mai ciki Æ™wajaja to ba za a yi layya da ita ba domin tana cikin marasa lafiya. Duba Sirãjus Sãliki [2/9-10] da Amuntaƙã [4/153].
Akwai wasu abubuwa na aibi da aka ambata da suke hana a yi layya da dabbar da take da su, amma akwai saɓanin a kansu, shi yasa na kawar da kai daga ambatonsu, domin magana mafi inganci shi ne; basa hana a yi layya da dabbar da take ɗauke da su.
Mustahabbi ne ga wanda zai yi layya ya nisanci yanke ƙumba (farce) da yin askin gashin jikinsa daga ranar ɗaya gawatan Zul-hijja izuwa ranar sallah. Duba Muktasarul IKalil [shafi na 123] da sharhinsa Al-Ikhlilu [1/301] da Jawãhirul Iklil [1/221]
Wasu malaman suna ganin har wanda za a sanya shi a layya ba zai aske kowanne gashi na jikinsa ba ko farcensa. Duba Bulgatus Sãliki [1/287] da Hãshiyatus Sãwi Ala Assharhi Assagir da aka buka tare da Assharhu Assagir [2/341]
Mu haÉ—u a rubutu na 4
Nuhu Ubale Ibrahim
(ABU RAZINA PAKI)
10/12/1442
Bugu na biyu