Biyo bayan gagarumar gudummawar da yake bayarwa a Jaridar LEADERSHIP Hausa wajen gabatar da darussan addini a shafin Dausayin Musulunci tun daga 2014, Mahukuntan Kamfanin LEADERSHIP sun mika takardar yabo da godiya ga Shehu Isma’il Umar Almadda da aka fi sani da “Mai Diwani”, a zawiyyarsa da ke Tudun Wada, Kaduna.
Mahukunta kamfanin sun ce babu shakka Shehu Isma’il Umar Almadda, ya zama zakaran gwajin dafi wajen jajircewarsa kan kula da shafin na tsawon shekaru akalla 10, wanda hakan ya sanya suka mika masa takardar jinjina da yabo a kan namijin kokarinsa.
- Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL
- Ba Za A Iya Dakatar Da Dunkulewar Kasar Sin Ba
Babban Editan LEADERSHIP Hausa, Abdulrazak Yahuza Jere, ne ya mika takardar yabon a madadin hukumar gudanarwar kamfanin LEADERSHIP.
Mika takardar yabon, ta zo daidai da ranar bude tafsirin watan Ramadana wanda Shehu Isma’il Umar Almadda yake gabatarwa a duk shekara a Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group da ke Tudun Wada, cikin Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna a makon da ya gabata.
Da yake jawabi kafin mika takardar, Babban Editan, ya jaddada muhimmancin rubutun da Shehu Isma’il Umar Almadda yake yi na ilmantar da al’umma a bangaren daban-daban da suka shafi addinin Musulunci tare da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da cewa a duk Juma’a shafin Dausayin Musulunci yana fita ba tare da fashi ko sau daya ba, don haka ya ce ya ce lallai wannan abin a yaba ne.
“Ba mu taba samun marubuci da ya jima yana ba da gudunmawa a LEADERSHIP Hausa kamar Shehu Isma’ila Umar Almadda ba. Karatuttukan da yake gabatarwa sun samu karbuwa a wurin jama’a bisa irin sakonnin da ake aiko mana a kai. Tun daga kan tarihin Annabi (SAW) da matsayinsa a wurin Allah da dabi’unsa da halayensa, da hukunce-hukuncen ibada da sauran karatuttukan da yake gabatarwa a shafin masu ilmantar ga al’umma sosai da kara wanzar da zaman lafiya. A madadin mahukuntan kamfaninmu, tun daga kan Shugaba, Madam Zainab Nda-Isaiah, da mataimakinta na farko, Azu Ishiekwene, da mataimaki na biyu, Mike Okpere da Manajan Darakta, Mu’azu Elazeh da Darktan Tarurruka, Abraham Nda-Isaiah da dukkan sauran mahukunta da manya da kananan ma’aikatan Kamfanin LEADERSHIP Group Limited, muna godiya.” In ji Abdulrazak.
A nashi bangaren, Shehu Isma’il Umar Almadda ya bayyana gamsuwarsa bisa karramashi da Kamfanin LEADERSHIP ya yi masa. Ya yi alkawarin ci gaba da bayar da gudummawarsa wajen ilmantar da al’umma kan lamuran da suka shafi addinin Musulunci.
Tun da farko, da yake bude tafsirin na bana, Shehu Isma’il Umar Almadda, ya dauki lokaci yana bayani kan sirrorin Alkur’ani mai girma da falalarsa da kuma addu’o’in samun zaman lafiya da kawar da kuncin rayuwa a Nijeriya da dukkan sauran kasashen duniya musamman Falasdin da Isra’ila take muzguna musu.
Malamai daga wurare daban-daban sun samu halartar bude tafsirin shehin na bana.