Idris Aliyu Daudawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KIWON LAFIYA

Likitoci Sun Bayyana Hanyoyi 10 Na Kiyayewa Don Kaucewa Cutar Mantuwa

by Idris Aliyu Daudawa
January 31, 2021
in KIWON LAFIYA
2 min read
Likitoci Sun Bayyana Hanyoyi 10 Na Kiyayewa Don Kaucewa Cutar Mantuwa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Sakamakon binciken da wasu likitocin kasar Amurka suka yi ya nuna cewar amfani da man zaitun musamman ma wajen girki yana taimakawa wajen inganta lafiyar kwakwalwa.
Binciken ya nuna cewar shi man zaitun baya daskarewa a jikin mutum kamar kitse wato ‘Protein Tau’ wanda likitoci suka ce yana haddasa cutar mantuwa wato ‘Dementia’.
Likitocin sun kuma gano cewar man zaitun na kara lafiyar jijiyoyi a jiki da kuma kwakwalwa.
Bugu da kari kuma yana kara kyan fata da kuma tsawon gashin kai.
Bayanai sun nuna cewar yawan cutar mantuwa ba wai ta tsaya bane lalle sai ga tsofaffi ba yanzu har ma da kananan yara suna kamuwa da ita cutar.
Sakamakon hakan ne yasa su masana suka yi wani nazari kan haka da gano abubuwan, da za su iya sa mutum ya rage yawan yin mantuwa.
A binciken na masannan da suka fara yi sun gano cewar shan kayan zaki kamar su alawa, cingam, chakulet da sauran su na taimakawa wajen kara kaifin kwakwalwa.
Da yake wasu ba za su iya mu’amala da wadannan kayan zaki ba, an zurfafa bincike bane domin gano wasu hanyoyin.
Hanyoyin dai sun hada da;
Samun isasshen barci sai kuma yin barci a lokacin da ya kamata.
Yin hirar zuci amma ba ko wanne lokaci ba, domin yawan yin hakan na iya sa mutum ya sami matsala a kwakwalwar sa.
Yin hira da mutane musamman abokan arziki.
Motsa jiki kamar su guje-guje da dai sauran su.
Tsayawa a hasken rana wanda ke bada Sinadarin ‘bitamin D’ bayan nan kuma da cin kayayyakin lambu ko abinda aka fi sani da ganyaryaki.
Yin wasannin da suke taimakawa wajen wasa kwakwalwa kamar chess, Sudoku, lissafi da dai sauran su.
Yin aiyukkan da ba a saba yi ba ko kuma ba a taba yi ba, da kuma ziyarar wuraren da ba a taba zuwa ba.
Yawan yin dariya wanda haka ya ke kawar da damuwa da dowewar kwakalwa.
Cin kayayyakin lambu musamman wadanda ake da kira da suna‘Bule Berries’ domin suna dauke ko kuma sun kunshi sinadarorin da suke taimakawa wajen hana ita cutar mantuwa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Bayan Canza Hafsoshin Tsaron Kasa, Sai Kuma Me?

Next Post

Muhammad Danjuma Katsina Gwarzon Dan Jarida A 2020.

RelatedPosts

Ciwon

Yanzu Ciwon Sikari Bai Bar Kowa Ba

by Idris Aliyu Daudawa
15 hours ago
0

Likita, wanda yake lura da masu fama da ciwon sikari...

Hawan Jini

Hawan Jini Ne Sanadiyar Mutuwar Kashi 20 Na Mutanen Duniya

by Idris Aliyu Daudawa
15 hours ago
0

Dr. Ojji Dike, wanda kwararren masanin cutar da ta shafi...

Ciwon Kai

Magungunan Ciwon Kai A Gargajiyance

by Idris Aliyu Daudawa
2 days ago
0

  KANUMFARI: Wanda yake fama da ciwon kai irin na...

Next Post
Muhammad Danjuma Katsina Gwarzon Dan Jarida A 2020.

Muhammad Danjuma Katsina Gwarzon Dan Jarida A 2020.

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version