Liverpool ta lashe gasar Premier League bayan ta farfaɗo daga ƙwallon farko da aka sanya mata a daga inda har ta doke Tottenham Hotspur 5-1 a filin wasa na Anfield a ranar Lahadi
Dominic Solanke ya kiɗima masoya na gida lokacin da ya zura ƙwallo a raga a minti na 12.
Liverpool ta mayar da martani da ƙwallaye uku kafin hutun rabin lokaci ta hannun Luis Diaz, Alexis Mac Allister da Cody Gakpo.
Mohamed Salah ya ƙara wa Liverpool ƙwallo ta huɗu a minti na 63. Haka kuma ƙwallon cin kai (own goal) ta Tottenham, Destiny Udogie, wacce ta koma cikin ragarsu ta ƙara sanyaya gwiwarsu.
Liverpool, wanda yanzu ta zama ta 20 a cikin tarihin lashe kyautar Premier League, tana da maki 82 daga wasanni 34 da aka buga, inda Arsenal ke a matsayi na biyu da maki 67.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp