Gamayyar Kungiyoyin Arewa 593 daga jihohi 19 na Arewacin Nijeriya sun bay-yana cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen matsalar musguna wa Fulani Makiyaya a fadin kasar nan.
Shugaban kungiyar na kasa, Dakta Awwal Abdullahi Aliyu ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron kungiyar da kungiyoyin Fulani da sauran kungiyoyi daga fadin Nijeriya wanda ya gudana a Jihar Kaduna.
- Ku Je Ku Magance Matsalar Yunwa Da Ta Addabi Jama’a -Fintiri
- Za Mu Ci Gaba Da Aiwatar Da Abubuwan Da Suka Sa LEADERSHIP Ta Karrama Mu – Gerawa
Shugaban ya ce kungiyarsu ta himmatu wajen tabbatar da cewa an daina mus-guna wa Fulani. Ya ce suma mutane ‘yan kasa kamar kowa.
“Mun gudanar da wannan taro ne domin tattauna matsalolin mutanenmu daga Arewa da kuma ‘yan Arewa da ke zama a kudancin kasar nan mu ga yadda za a zauna lafiya, wadanda aka zalunta mu ga ta ya ya za a yi a kwato musu hakkinsu, sannan a hukunta wadanda suka yi zuncin.
“Mun shiga gaba wajen ganin yadda za a warware bakin fentin da aka shafa wa Fulani, wanda ake ganin kowanne Bafulatani dan ta’adda ne ko dan garkuwa da mutane ne saboda rashin adalci na yi wa al’umma guda daya jam’u wanda bai kamata ba.
“Kungiyarmu ta himmatu wajen tattaunawa da gwamnati mu ga yadda za a warware matsalar da ke tsakanin Fulani.”